Tukin ganganci: An gurfanar da direban da ya tare tawagar Osinbajo

Tukin ganganci: An gurfanar da direban da ya tare tawagar Osinbajo

An gurfanar da wani direban babbar mota mai suna Abubakar Musa mai shekaru 43 a gaban wata kotun majistare da ke Ikeja. Ana zarginsa ne da tukin gangancin da ya yi sanadin tare tawagar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo a Legas.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Samuel Mishozumu, ya zargi mai kare kansa kuma mamallakin mota mai lamba LND 976 XF, da tukin ganganci a kan babbar hanya. Hakan yayi sanadin hana tawagar mataimakin shugaban kasa wucewa.

“Mai kare kansa din ya ki bin dokokin kan titin kuma ya tuka babbar motarsa har ta shigewa tawagar. Kokarin jami'an tsaron tawagar na ganin sun kaucewa hakan ya tashi a tutar babu,” ya ce.

Tukin ganganci: An gurfanar da direban da ya tare tawagar Osinbajo
Tukin ganganci: An gurfanar da direban da ya tare tawagar Osinbajo
Asali: Twitter

Mishozumu ya sanar da kotun cewa, wanda ake karar ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Janairu da wajen karfe 10:15 na dare a kan babban titin Oshodi Apapa, Oshodi, a jihar Legas.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje, 'yan majalisa da sarakuna sun kai wa Buhari ziyara (Hotuna)

Wannan laifin kamar yadda yace, ya ci karo da tanadin sashi na 19, sakin layi na daya da kuma sashi na 45 na dokokin kan titin jihar Legas, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Alkalin kotun, Mai shari’a O. D. Njoku ya amince da bada belin wanda ake zargin a kan naira dubu hamsin da kuma tsayayyu mutum biyu.

Njoku ya bada umarnin cewa dole tsayayyun su zama masu aikin yi. Daga nan ya dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Fabrairu na 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel