Bruce McConville: Mutumin da ya kone dala miliyan daya, saboda baya so ya biya tsohuwar matarshi kudin kula da yaransu

Bruce McConville: Mutumin da ya kone dala miliyan daya, saboda baya so ya biya tsohuwar matarshi kudin kula da yaransu

- Bruce McConville dan kasuwa ne a kasar Canada wanda yayi ikirarin ya kone makuden kudi har dala miliyan daya

- Ya yi hakan ne don kada ya biya matar kasonta na kasuwancin da suka kafa tare har suka tara kadarori kafin rabuwarsu

- Wanda ake karar ya ce tsananin fushi ne yasa yayi hakan kuma bai ko musanta aikatawa ba a gaban alkalin

Bruce McConville dan kasuwa ne a kasar Canada. An ruwaito cewa ya kona kudin tsohuwar matarshi ne don kada ya biya dala miliyan daya na kudin sakin da ya shiga tsakaninsu.

Kamar yadda Ottawa Citizen suka ruwaito, dan kasuwan mai shekaru 55 ya yi wannan ikirarin ne a gaban wata babban kotu.

A yayin zaman kotun da aka yi makon da ya gabta, ya bayyana cewa ya siyar da kadarorin da kuma kasuwancin da suka kafa tare da tsohuwar matarshi kafin su rabu, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Bruce McConville: Mutumin da ya kone dala miliyan daya, saboda baya so ya biya tsohuwar matarshi kudin kula da yaransu
Bruce McConville: Mutumin da ya kone dala miliyan daya, saboda baya so ya biya tsohuwar matarshi kudin kula da yaransu
Asali: Facebook

Ya yi bayanin yadda ya siyar da kadarorin tare da kwashe dala miliyan daya kafin ya banka musu wuta cikin fushi. Ya ki bin umarnin kotun wacce ta haramta mishi siyar da kadarorin.

Ya kara da cewa duk da ya karba shaida daga ATM amma yanzu ba ya tare da kudin. A take alkalin ya tambaya “A yanzu ina kudin suke?” McConville ya sanar da alkalin cewa ya kona kudin.

KU KARANTA: Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Balarabiya ‘yar kasar Saudiyya tayi ridda ta bar addinin Musulunci

A take kuwa alkalin cikin dimuwa ya ce, “Ka rasa ni gaskiya. Ta yaya kake son in kare ka? Da kace ka kona, me kake nufi?”

Abinda ya ba kowa mamaki shine yadda ya bayyana cewa ya kone kudin. Wannan martanin ya jawo sauran zafafan tambayoyi daga alkalin zuwa wanda ake tuhumar.

Bayan kammala sauraron dukkan bangarorin tare da tabbatar da cewa ya kurmushe kudin da suka tara da matar tashi, alkalin ya yanke mishi hukuncin kwanaki 30 a gidan gyaran hali don jan kunne. Alkalin ya kara da cewa. A zama na gaba na kotun, matukar bai fito ya sanar da sahihin zancen ba, zai fuskanci hukuncin mai zafi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel