Yanzu-yanzu: Bamu bukatar shege-ka-fasa a jihar Kano - Ganduje

Yanzu-yanzu: Bamu bukatar shege-ka-fasa a jihar Kano - Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta nisanta kanta daga sabuwar shirin tsaron da matasan Arewa suka kafa mai suna 'Shege-ka-fasa'.

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a yayinda yake hira da manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawar jigogin APC na Kano da shugaba Muhammadu Buhari.

Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta zuba kudade wajen tabbatar da tsaro a dukkan sassan jihar kuma basu bukatar wata kungiyar tsaro.

Yanzu-yanzu: Bamu bukatar shege-ka-fasa a jihar Kano - Ganduje
Ganduje
Asali: Facebook

KU KARANTA: Ban taba kira Buhari mai tsattsaurin ra'ayin addini ba - Tinubu

Mun kawo muku rahoton cewa Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar a ranar Alhamis ya ce sakacin 'yan bokon arewa ne yasa wasu matasan yankin suka kirkiri wata rundunar tsaro da suke kira 'Operation Shege Ka Fasa.'

Ya bukaci shugabanin yankin na Arewa su ja kunnen matasan.

Sultan din ya yi wannan jawabin ne a yayin taron tsaro na Arewa da aka gudanar a Kaduna a ranar Alhamis.

Hadakar kungiyoyin Arewa ta fitar da tambari da motocci na rundunar tsaron a ranar Laraba a Kaduna.

Sultan ya ce, "Na gani a talabijin kuma kafafen watsa labarai na ta yada abin. Dattawa ne suka bari matasa su kafa abin. Saboda haka 'yan bokon mu da jagororin mu ne matsalar mu. Idan manyan mu ba su shika harkar ba, matasan za su iya aikata duk abinda suka ga dama. Ya kamata a rika jan kunnen matasa tare da yi musu jagora.

"Yanzu sun kafa rundunar tsaron su ni ban fahimci sunan da suke kiransa ba, mene Shege Ka Fasa ya ke nufi?

"Ina kira ga dattijan arewa su ja musu kunne. Kada ku bari matasa su kwace shugabanci daga hannun ku. Ya kamata ku rika tuntubar mutane duk matsayinsu. Ina ganin akwai bukatar mu fuskanci lamarin kada mu bari matasa su dauki komi a hannunsu. Ina ganin ya kamata mu kara dage wa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel