Ban taba kira Buhari mai tsattsaurin ra'ayin addini ba - Tinubu

Ban taba kira Buhari mai tsattsaurin ra'ayin addini ba - Tinubu

Babban jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya ce ba shi yayi jawabin da ke siffanta shugaba Muhammadu Buhari matsayin mai tsattsaurin ra'ayin addini ba

Wani rahoto da ya yadu a kafafen Soshiyal Midiya na cewa a 2003, lokacin da Tinubu ke gwamnan jihar Legas, ya siffanta Buhari a matsayin dillalin raba kan al'umma, mai tsattsaurin ra'ayin addini kuma mai tsananin nuna kabilanci.

A rahoton, an ce Tinubu ya ce "Muhammadu Buhari dillalin raba kan al'umma ne, mai tsattsaurin ra'ayin addini kuma mai tsananin nuna kabilanci ne. Idan aka bashi daman shugabantan kasar nan, sai ya raba kan kasar."

"Halin nuna kabilancinsa zai kawo cikas wajen hadin kan Najeriya."

Ban taba kira Buhari mai tsattsaurin ra'ayin addini ba - Tinubu
Ban taba kira Buhari mai tsattsaurin ra'ayin addini ba - Tinubu
Asali: Twitter

A 2003, Buhari ya yi takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP), a lokacin kuma, Tinubu ya yi takaran kujeran gwamnan jihar Legas karkashin jam'iyyar Alliance for Democracy (AD).

Mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, a jawabin da ya saki ranar Juma'a ya karyata rahoton kuma ya ce wannan aikin masu yada labarun bogi ne.

Ya ce Tinubu bai taba irin wannan magana ba kan Buhari kuma yana kira ga jama'a suyi watsi da rahoton.

Rahman ya kalubalanci wadanda ke yada maganan su kawo hujjan inda Tinubu ya fadi hakan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel