Tashin hankali: Alade ya sha giya kwalba shida ya bugu yaje ya tsokano Sa sun dambatu

Tashin hankali: Alade ya sha giya kwalba shida ya bugu yaje ya tsokano Sa sun dambatu

- Wani katon Alade a kasar Australia ya ba mutane mamaki yayin da ya sha pakitin giya har shida

- Bayan tsananin buguwar da yayi, ya je ya toskano Sa da fada inda suka dinga gudu a kan titi

- Daga bisani Aladen ya fada rafi inda ya dinga iyo har zuwa gabar kafin ya fadi kasan wata bishiya ya fara bacci

Wani katon Alade wanda ya sha giya ya bugu ya fada titi yana ta hauka, inda daga bisani ya je ya fara fada da Sa.

Babban Aladen ya sha giya ne bayan ya sato ta. Ya bugu sosai bayan ya sha pakiti shida mai kunshe da giya uku a cikin duk pakiti daya. Ya balle ne daga mazauna kusa da rafin da ke sansanin DeGrey a Port Hedland a Australia.

A abin mamakin da ya faru, dabbar ta je bola ne da farko inda ta fara dube-dube kafin daga bisani ta je tare da fara kirkirar fada da wani Sa da ke gefe, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Daga nan, Aladen ya yanke hukuncin yin iyo kafin ya kai ga gaba inda ya fadi a karkashin wata bishiya tare da fara bacci.

KU KARANTA: Iyaye 'yan Najeriya sun tsinewa 'yarsu da ta gudu kasar Canada ta zama 'yar madigo

Daya daga cikin ‘yan sansanin mai suna Merida ta sanar da ABC network yadda lamarin ya faru: “Da tsakar dare ne wasu suka ji motsin gwangwanaye. Suna fita tare da haskawa sai suka ci karo da Alade yana fasa gwangwanayen. Daga nan ne ya je ya fara watsa dattin da aka rufe.

“Akwai wasu mutane da ke can wajen rafi. Kawai sun gan shi yana biye da wani abin hawa ashe fada ya ja Sa da shi. Daga nan sai ya fada rafin tare da yin iyo zuwa gabar. Ya fadi kasan wata bishiya inda ya bige da bacci.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel