Gwamnatin Buhari za ta fara sayar da gidaje 1,094 da ta gina a jahohi 35

Gwamnatin Buhari za ta fara sayar da gidaje 1,094 da ta gina a jahohi 35

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta fara sayar da gidajen da ta kammala ginasu guda 1,094 a babban birnin tarayya Abuja da kuma jahohi 34 dake fadin kasar nan, nan nada jimawa ba.

Hadimin shugaban kasa a kan harkokin watsa labaru, Femi Adesina ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a, inda yace aikin gina gidajen ya samar da ayyukan kai tsaye guda 455,048.

KU KARANTA: Cika shekaru 45 a karaga: Abubuwa 18 da ya kamata ku sani game da Sarkin Zazzau

Adesina yace ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola ne ya bayyana haka yayin da yake gabatar da bayanin ayyukan ma’aikatarsa na shekarar 2019, inda yace daga cikin aikin da aka bashi akwai gina gidaje 200,000 a kowanne shekara.

“Gwamnatin Buhari ta mayar da hankali wajen samar da manyan ayyukan more rayuwa da suka hada da tituna, gadoji, layin dogo, wutar lantarki, filin sauka da tashin jirage, gidahe da sauransu, kuma a shirye take ta cimma wannan buri.

“Game da gidaje, mun kammala aikin gina fiye da gidaje 1,094 a duk fadin kasar nan a rukunin farko na aikin, kuma muna cigaba da aiki a jahohi 34 har da babban birnin tarayya Abuja. Nan bada jimawa ba zamu fitar da tallar gidajen.” Inji shi.

A wani labarin kuma, gwamnatin jahar Kaduna, a karkashin jagorancin Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ta kwace wani tsohon Hotel, Durbar Hotel, mallakin iyalan tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha dake kan titin Muhammadu Buhari Way a birnin Kaduna.

Gwamna ya bayyana cewa sun kwace kadarar ne sakamakon hukumar Hotel din bata biyan harajin kasa tsawon shekaru 19, duk da cewa wata babbar kotu dake zamanta a Kaduna ta hana gwamnatin rusa Otal din da kwace shi a hukuncin da ta yanke a ranar 21 ga watan Janairu.

Sai dai dai ciki wata wasika dake dauke da kwanan wata 31 ga watan Disambar 2019, wanda aka gwamnati ta aika ma dan Abacha, Mohammed Abacha ta sanar ma iyalan Abacha cewa ta kwace kadarar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel