Iyaye 'yan Najeriya sun tsinewa 'yarsu da ta gudu kasar Canada ta zama 'yar madigo

Iyaye 'yan Najeriya sun tsinewa 'yarsu da ta gudu kasar Canada ta zama 'yar madigo

- Iyalan Shoremi da ke jihar Ogun sun sallama ‘yar su mai suna Shalom da ke zama a kasar Canada

- Shalom ta garzaya gaban wata babbar kotu ne da bukatar auren mace ‘yar uwarta a matsayinta na ‘yar madigo

- Danginta sun bayyana cewa sun sallamawa duniya ita kuma suna tabbatar da cewa ba ta da gadon ko tsinke daga garesu

Iyalan Shoremi daga jihar Ogun sun sallamawa duniya wata ‘yar su mai yin madigo da ke zama a kasar Canada. Iyalan sun bayyana cewa sun sallama Shalom ne bayan da suka gano ta fara neman yardar kotu don ta auri wata mace.

Kamar yadda dangin Shalom suka gani, kotun tayi watsi da wannan bukatar yayin da ta dogara da haramcin auren jinsi na 2014, kamar yadda haridar Gistmania ta ruwaito.

Iyaye 'yan Najeriya sun tsinewa 'yarsu da ta gudu kasar Canada ta zama 'yar madigo
Iyaye 'yan Najeriya sun tsinewa 'yarsu da ta gudu kasar Canada ta zama 'yar madigo
Asali: Facebook

Wannan dokar kuwa ta haramta auren jinsi a Najeriya kuma ta yanke hukuncin shekaru 14 a gidan gyaran hali ga wadanda aka kama da laifin mu’amalar jinsi daya.

Duk da wannan dokar da kasar nan ta kafa, Shalom ta yanke hukunci zuwa gaban kotu neman lasisi. Lamarin da yasa iyayenta suka bayyana cewa sun sallamata.

KU KARANTA: An kashe dan Najeriya saboda kawai yayi fitsari akan titi a kasar Amurka

Kamar yadda suka wallafa mujalla kuma jaridar Gistmania ta gani, “Hankalin iyalan Shoremi ya kai ga wata bukatar auren jinsi daya da Shalom T. Shoremi ta mika gaban kotu. Ta bukaci babbar kotun jihar da ta amince mata ta auri mace ‘yar uwarta. Kotun tayi watsi da wannan bukata don kuwa ta take dokar hana auren jinsi daya na Najeriya.

“Danginta na nesanta kansu da wannan bukatar ta ta kuma suna sanar da cewa sun tsinke duk wata alakar da ke tsakaninsu. Sun tsinke zumuncin ne saboda tana shirya aikata abinda yayi karantsaye ga dokar Najeriya. A don haka ne ba ta da gadon danginta.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng