Sanata Bulus Amos ya nada hadimai 118, ya fadi dalili

Sanata Bulus Amos ya nada hadimai 118, ya fadi dalili

- Wani sanatan Najeriya, Bulus Amos mai wakiltan Gombe ya nada hadimai 118 daga gundumomi arba'in a mazabarsa

- Sanatan ya ce ya nada mutane da yawa ne domin tallafawa matasa da rage zaman banza da tayar da zaune tsaye

- Amos ya ce ya nada mataimaka biyu daga kowanne mazaba da kuma mataimaka na musamman 38

Bulus Amos, Sanata mai wakiltan mazabar Gombe ta Kudu ya bayyana cewa ya nada hadimai 118 daga gundumomi arbain da ke mazabarsa.

Sanatan ya bayyana hakan ne cikin wata sako da mai magana da yawun sa, Abdul Lauya ya fitar a ranar Alhamis 6 ga watan Fabrairu kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatan Najeriya ya nada hadimai 118, ya fadi dalili
Sanatan Najeriya ya nada hadimai 118, ya fadi dalili
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An kama 'yar sanda da ta yi ta murde mazakutar wani makanike a caji ofis

Sanatan ya ce wadanda ya nada a matsayin hadimansa za su rika jiyo koken talakawa suna fada masa domin ya share musu hawaye.

Ya ce wadanda ke riƙe da mukamin mataimaka na musamman za su rika wakilan kungiyoyi na musamman kamar na mata, matasa, dalibai, masu bukata ta musamman da dattijai ta ofishinsa da ke Bambam.

A wani rahoton, Kakakin Majalisar Najeriya Femi Gbajabiamila da shugaban kwamitin tsaro, Babajimi Benson sun nuna damuwarsu kan yadda wasu kasashen ketare da naukan nauyin ta'addanci a kasar.

A cewar The Nation, an bayyana hakan ne bayan 'yan Majalisar sun yi taro da shugabanin hukumomin tsaro a ranar Laraba 5 ga watan Fabrairu bayan da hankulan mutane a kasar ke cigaba da tashi saboda kallubalen rashin tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel