An kashe dan Najeriya saboda kawai yayi fitsari akan titi a kasar Amurka

An kashe dan Najeriya saboda kawai yayi fitsari akan titi a kasar Amurka

- Wani mai daukan hoto mai suna Rasheed O.J Olabode ya sheka lahira bayan da wani dan kasar Amurka ya harba mishi harsashi a zuciya

- Dan asalin kasar Amurkan mai suna Christopher Poole ya kashe Olabode ne saboda yayi fitsari a gefen wata mota da ke kan titin Newark a Amurka

- Alkalin babbar kotun da ya yanke hukuncin,, ya ce bai taba samun kisan rashin tausayi ba da kuma ganganci kamar wannan

An gano cewa wani mai daukan hoto dan asalin Najeriya mai suna Rasheed, wanda aka fi sani da O.J. Olabode ya mutu. Wani mutum mai suna Christopher Poole mai shekaru 26 ne ya kashe shi a wani titin kasar Amurka saboda yayi fitsari a gefen titin.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Christopher Poole ya kashe saurayin mai shekaru 27 ne ta hanyar harbin shi da bindiga a zuciyarshi bayan da saurayin ya roki gafarar shi.

Christopher ya ga Olabode ne yana fitsari a gefen wata mota a Newark a watan Afirilu 2018, lamarin da ya ja ya tunkareshi.

Kamar yadda kamarar kan titi ta nuna, Olabode ya roki makashin nashi a kan ya hakura ya kyaleshi amma sai Poole ya ki.

“Laifin da wanda aka kashe din yayi shine yin fitsari a gefen motar,” dan sanda mai gabatar da kara Jason Goldberg ya sanar da kotun yankin Essex.

KU KARANTA: Mai yayi zafi: Miji ya kashe matarsa ya binne gawarta a cikin dakinsu

“Amma kuma wannan karamin laifi ne wanda kowa zai iya yi. Hakazalika ya roki Poole a kan ya kyaleshi tare da neman yi mishi bayani amma sai ya harbe shi a zuciya.” Ya kara da cewa.

Bayan kammala sauraron kowanne bangare, alkalin babbar kotun mai suna Ronald Wigler ya yanke wa Poole hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Bayan lura da yayi da rashin dana-sanin da Poole ya nuna, ya ce: “A gaskiya wannan ne shari’ar kisa ta rashin hankali da ta taba zuwa gabana.”

A ranar Talata, 4 ga watan Fabrairu, an yanke wa Poole hukuncin daurin rai da rai. An kara mishi da shekaru 10 a gidan yarin saboda samun shi da aka yi da makami, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito

Olabode dan asalin Najeriya ne kuma ‘yan uwanshi ba su samu halartar zaman kotun ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel