Cika shekaru 45 a karaga: Abubuwa 18 da ya kamata ku sani game da Sarkin Zazzau

Cika shekaru 45 a karaga: Abubuwa 18 da ya kamata ku sani game da Sarkin Zazzau

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris zai cika shekaru 45 a kan karagar mulki a ranar Asabar, 8 ga watan Feburairu na shekarar 2020 tun bayan darewarsa a matsayin Sarkin Zazzau na 18.

Daily Trust ta ruwaito Ciroman Shantalin Zazzau, Alhaji Abubakar Ladan ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, inda yace za’a gabatar da addu’o’i, hawan daba da sauran hidimomi don taya mai martaba Sarki murna.

KU KARATA: Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3

Cika shekaru 45 a karaga: Abubuwa 18 da ya kamata ku sani game da Sarkin Zazzau
Cika shekaru 45 a karaga: Abubuwa 18 da ya kamata ku sani game da Sarkin Zazzau
Asali: Facebook

“Kimanin hakiman Sarki 44 da manyan yan fada ne zasu shiga cikin hawan daba da za’a gudanar, haka kuma za’a gabatar da addu’o’i a ranar Juma’a a babban Masallacin fadar Sarki da sauran masallatan dake masarautar.” Inji shi.

Masarautar Zazzau ta kai tsawon shekaru 1000, amma jahadin Shehu Usmanu Dan Fodio a shekarar 1804 ya kawo sabon shafi a tarihin masarautar, kuma tun daga wannan lokaci zuwa yanzu babu Sarkin da ya kwashe shekaru 45 a kan mulki sai Shehu Idris.

Legit.ng ta kawo muku wasu muhimman bayanai 18 game mai martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris:

- A ranar 20 ga watan Feburairu 1936 aka haifi Sarki Shehu Idris

- Shekarun Sarkin Zazzau Shehu Idris 83

- Sunan mahaifin Sarki Malam Idris Autan Sambo

- Sunan mahaifiyar Sarki Hajiya Aminatu

- A ranar 8 ga watan Feburairu 1975 aka nada shi Sarkin Zazzau

- Sarki Shehu Idris ya gaji Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu

- Sarki Shehu Idris ne Sarki na 18 a masarautar Zazzau

- Mahaifin Sarki Shehu Idris ya rasu yana dan shekara 12

- Kakansa da Kakan babansa dukkaninsu sun yi sarautar Zazzau

- Kakansa, Sarki Muhammadu Sambo ya mulki Zazzau daga 1879 zuwa 1888

- Kakan babansa, Sarki Abdulkarimi ya mulki Zazzau daga 1834 zuwa 1846

- Sarki Shehu Idris ya yi karatun ilimentari daga 1947 zuwa 1950

- Sarki Shehu Idris ya yi makarantar Zaria Midil daga 1950 zuwa 1955

- Sarki Shehu Idris ya yi karatu a makarantar horas da malamai ta Katsina

- Sarki Shehu Idris ya koyar a Hunkuyi a shekarar 1958

- Sarki Shehu Idris ya zama sakataren Sarki Aminu a shekarar 1960

- Sarki Shehu Idris ya zama sakataren hukumar mulki ta Zaria a 1965

- Sarki Shehu Idris ya zama Dan Madamin Zazzau a shekarar 1973

Mu ma a nan muna taya mai martaba Sarki murnar cika shekaru 45, tare da fatan Allah Ya kara masa lafiya da nisan kwana. Allah Ya ja zamanin Sarki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel