Sarkin Musulmi ya yi gargadi a kan rundunar tsaro ta Shege-Ka-Fasa

Sarkin Musulmi ya yi gargadi a kan rundunar tsaro ta Shege-Ka-Fasa

Sarkin musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar a ranar Alhamis ya ce sakacin 'yan bokon arewa ne yasa wasu matasan yankin suka kirkiri wata rundunar tsaro da suke kira 'Operation Shege Ka Fasa.'

Ya bukaci shugabanin yankin na Arewa su ja kunnen matasan.

Sultan din ya yi wannan jawabin ne a yayin taron tsaro na Arewa da aka gudanar a Kaduna a ranar Alhamis.

Hadakar kungiyoyin Arewa ta fitar da tambari da motocci na rundunar tsaron a ranar Laraba a Kaduna.

Sarkin Musulmi ya yi gargadi a kan rundunar tsaro ta Shege-Ka-Fasa
Sarkin Musulmi ya yi gargadi a kan rundunar tsaro ta Shege-Ka-Fasa
Asali: Twitter

Sultan ya ce, "Na gani a talabijin kuma kafafen watsa labarai na ta yada abin. Dattawa ne suka bari matasa su kafa abin. Saboda haka 'yan bokon mu da jagororin mu ne matsalar mu. Idan manyan mu ba su shika harkar ba, matasan za su iya aikata duk abinda suka ga dama. Ya kamata a rika jan kunnen matasa tare da yi musu jagora.

"Yanzu sun kafa rundunar tsaron su ni ban fahimci sunan da suke kiransa ba, mene Shege Ka Fasa ya ke nufi?

"Ina kira ga dattijan arewa su ja musu kunne. Kada ku bari matasa su kwace shugabanci daga hannun ku. Ya kamata ku rika tuntubar mutane duk matsayinsu. Ina ganin akwai bukatar mu fuskanci lamarin kada mu bari matasa su dauki komi a hannunsu. Ina ganin ya kamata mu kara dage wa."

Ya kuma bukaci gwamnonin jihohin arewa su magance kallubalen tsaro da ke adabar yankin.

Sultan ya kuma bayyana damuwarsa a kan marayu 50,000 da ke yankin sakamakon rikicin ta'addancin Boko Haram.

Ya ce idan ba a dauki matakin tallafawa marayun ba za su zama fitinar da ta fi na Boko Haram.

"An bayar da shawarwari da dama sai dai har yanzu ba a aiwatar da su ba, hakan na nufin za mu cigaba da fuskantar abinda zai biyo baya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel