Yadda 'yan sanda suka kama 'yan uwansu 'yan sanda da ke karbar cin hanci a Legas (Bidiyo)

Yadda 'yan sanda suka kama 'yan uwansu 'yan sanda da ke karbar cin hanci a Legas (Bidiyo)

Wani faifan bidiyo da ke yawo a dandalin sada zumunta na intanet ya nuna wasu jami'an 'yan sanda suna kama abokan aikinsu saboda laifin karbar cin hanci.

Jami'an 'yan sandan Najeriya ta runduna ta musamman na 'Operation Puff Adder' ne suka isa wurin da abin ke faruwa a cikin motarsu ta sintiri kuma suka kama 'yan sandan da ke karbar rashawar a unguwar Ijesha da ke Legas.

Kawo yanzu dai rundunar ta 'yan sanda ba ta ce wani abu a kan faifan bidiyon ba.

A kwanakin baya an taba samun wani bidiyon da ke nuna wani dan sandan da aka yi ikirarin yana amfani da na'urar POS na hada-hadar kudade domin karbar kudi daga hannun mutane.

DUBA WANNAN: Shege-Ka-Fasa: Arewa za ta kafa rundunar tsaronta na musamman (Hotuna)

Bidiyon wanda ya yi fice ya nuno dan sandan da ba a san kowanene ba rike da na’urar POS a hannunsa yayinda ya damke mutumin.

An jiyo jami’in cikin daga murya yana neman mutumin ya bashi katin ATM dinsa.

Batun karbar cin hanci lamari ne da ya dade yana ci wa 'yan Najeriya tuwa a kwarya. Kididiga da wata kungiya mai suna 'Transparency International’, ta yi ya nuna cewa 'yan sanda suna sahun farko cikin jerin hukumomin da aka fi cin hanci da rashawa a Najeriya.

Sauran hukumomin da rahoton da aka wallafa a Yulin 2019 ya lissafa sun hada da majalisar kasa da kuma fanin shari'a.

‘Transparency International’ ta ce munin cin hanci da rashawa a ne ya hana kasashen Afrika inganta tattalin arzikin su, inganta siyasa da kuma ci gaban rayuwan al’ummar su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel