Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3

Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ma matashin nan da ya tako a kasa daga jahar Katsina zuwa jahar Kano domin murnar nasarar da ya samu a kotun koli, kabakin alheri, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Wani hadimin gwamnan mai suna Fa’izu Alfindiki ne ya bayyana haka a shafinsa na dandanin sadarwar zamani na Facebook, inda yace gwamnan ta bakin mai magana da yawunsa Auwalu Anwar ya baiwa Nura manyan kyautuka guda 3.

KU KARANTA: Hukumar INEC za ta kirkiro sabbin rumfunan zabe kafin zaben gama gari na 2023

Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3
Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3
Asali: Facebook

Wadannan kyautuka sun hada da:

- Kyautan kujeran Makkah

- Kyautan kudi N500,000

- Kyautan na’urar kwamfuta ta Laptop

Mai magana da yawun Ganduje ya sanar da hakan ne yayin wata kasaitacciyar walima da aka shirya ma kwamared Nura Aliyu a fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Alhamis, 6 ga watan Feburairu, inda aka ci kuma sha.

A hannu guda kuma, mai martaba Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila ya yi ma Nura mai tattaki nadin sarautar “Sarkin Zumuncin Rano” bisa kokarin da ya yi ya tako takanas ta kano daga jahar Katsina zuwa Kano a kasa.

Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3
Gwamna Ganduje ya gwangwanje Nura mai tattaki da manyan kyautuka guda 3
Asali: Facebook

A wani labarin kuma, shahararren tauraro a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood, Sani Musa Danja ya zargi gwamnatin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da rufe wani sabon kamfaninsa saboda bambancin siyasa dake tsakaninsu.

Danja ya zargi gwamnatin Ganduje ta hannun hukumar tace fina fina a jahar Kano ta rufe masa kamfanin da ya bude na daukan hotuna saboda siyasa, sai dai hukumar ta musanta wannan zargi, inda tace jarumin bai yi ma kamfaninsa rajista ba.

Tun ba yau ba, Sani Danja ya yi suna wajen goyon bayan jam’iyyar PDP da kuma tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, don haka baya tare da jam’iyyar APC da Gwamna Ganduje.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel