2023: INEC za ta kara adadin rumfunan zabe
Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana cewa za ta kara rumfunan zabe a fadin kasar nan kafin zuwan zaben shekarar 2023. Shugaban hukumar INEC din, Mahmood Yakubu ne ya sanar da hakan a takardar da daraktan ilimantar da masu zaben, Oluwole-Uzzi ya fitar a ranar Alhamis a garin Abuja.
Kamar yadda takardar ta sanar, Yakubu ya sanar da hakan ne yayin da ya karba GIS da kayan tallafin da cibiyar tallafawa zabe ta Turai, ECES ta mika wa Najeirya a garin Abuja a ranar Laraba.
Yakubu ya ce a halin yanzu Najeriya na da rumfunan zabe 119,973 ne tare da rassan rumfunan 57,000. Jimillar ya kama akwatuna 180,000 a fadin kasar.
Yakubu ya ce hukumar na hada guiwa da hukumar kidaya don samun cimma manufar samar da karin rumfunan zaben da zasu taimaka wajen saukaka zaben ga 'yan Najeriya da ke kara yawa.
DUBA WANNAN: Shege-Ka-Fasa: Arewa za ta kafa rundunar tsaronta na musamman (Hotuna)
Shugaban hukumar INEC ya mika godiya ga wadanda suka bada kyautar kayan aikin da zasu taimakawa wajen sauke hakkin hukumar zaben a saukake, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
"Taimakonku zai kara wa kokarinmu karfi ne. Hukumar na tunanin kirkiro da sabbin rumfunan zabe kafin zuwan zaben 2023. Najeriya babbar kasa ce kuma kullum kara yawa jama'arta suke yi. Duk lokacin muka zagaya kasar nan tare da kwamishinonin zaben, mu kan ci karo da sabbin wurare." in ji Yakubu.
"A koda yaushe muna tunanin yadda zamu kirkiri sabbin rumfunan zaben a irin wuraren don mu saukakewa 'yan Najeirya wahalar tafiya mai nisa don kada kuri'a," cewar Yakubu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng