Ganduje da Sanusi: Sarkin Ningi ya ba Buhari shawara

Ganduje da Sanusi: Sarkin Ningi ya ba Buhari shawara

Sarkin Ningi na jihar Bauchi, Alhaji Yunusa Danyaya, ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan ya tseratar da masarautar Kano daga wargajewa da gaggauwa. Ya roki shugaban kasan a kan ya saka baki a kan barakar da ke tsakanin Sarkin kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II da kuma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Basaraken ya yi wannan rokon a ranar Alhamis ne yayin tattauna da manema labarai a fadarsa da ke garin Ningi. Ya ce kiran ya zama dole ne idan aka dubi yadda wutar baraka ke ruruwa tsakanin sansui da Ganduje.

"Ina rokon shugaban kasa a matsayin uba ga kowa da ya duba girman Allah ya shiga cikin matsalar da ke tunkarar Kano kuma ya sasanta tsakanin Sarki da Gwamna. Ina da tabbacin cewa Buhari ba zai bar masarautar Kano ta tabarbare ba kuma a tozarta ta," ya yi kira.

Basaraken ya ce Buhari ya kasance mutum mai matukar girmama masarautun gargajiya. Ya kara da cewa: "Wannan ya zama dole mu kai kokenmu wajen mahaifinmu, uban kasarmu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Zai iya shawo mana kan matsalarmu saboda ya shawo kan matsalar da ta fi wannan a baya."

Ganduje da Sanusi: Sarkin Ningi ya ba Buhari shawara
Ganduje da Sanusi: Sarkin Ningi ya ba Buhari shawara
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Shege-Ka-Fasa: Arewa za ta kafa rundunar tsaronta na musamman (Hotuna)

Sarkin ya jajanta yadda duk kokarin manyan Najeriya na wajen ganin sun sasanta su, ya tashi a kawai. Ya kara da cewa a matsayinsa na daya daga cikin tsofaffin sarakuna mai shekaru 85 kuma yayi 42 a karagar mulki, dole ne yayi magana.

"Ba don ina goyon bayan sarkin Kano bane yasa nake magana. Ina magana ne saboda za a gurbata sarautar gargajiyar baki dayanta. A don haka ne nake ganin ya zama dole in yi magana a kan abinda na gani za a yi ba dai-dai ba." cewarsa.

Basaraken ya kara da yin bayanin cewa, duk abinda zai zama tozarci ga Sanusi an riga anyi shi. A don haka babu bukatar kin yafiya. "Idan mutum yayi ba dai-dai ba a musulunci, abinda muka sani shine a yafe masa. Idan Sanusi yayi ba dai-dai ba, me zai sa jama'a, gwamnatin Kano da majalisar jihar ba zasu yafe masa ba?" ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel