Boko Haram: A ba tsofaffin ‘Yan ta’adda sana’a ko jari – Shehu Sani

Boko Haram: A ba tsofaffin ‘Yan ta’adda sana’a ko jari – Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci jihar Kaduna a majalisar baya, ya yi kira ga gwamnatin tarayya game da lamarin ‘Yan ta’addan Boko Haram.

Shehu Sani ya tofa albarkacin bakinsa ne game da tsofaffin ‘Yan ta’addan da su ka tuba, kuma ake dawo da su cikin al’umma su sake sabuwar rayuwa.

Wasu sun soki lamarin, su na ganin wannan mataki na shigo da tubabbun ‘Yan ta’addan bayan an horas da su, ya na iya jagwalgwala sha’anin tsaro.

Tsohon Sanatan ya bukaci gwamnatin kasar ta tabbata cewa wadanda ake saki cikin al’umma sun samu abin da za su dogara da shi idan sun dawo gida.

A cewarsa, muddin wadannan Bayin Allah ba su samu hanyar samun kudi ba, akwai yiwuwar su iya komawa halin ta’addancin da su ka baro a baya.

KU KARANTA: Sharri Duniya ta ke yi wa Abacha na cewa ya saci kudi - CSO

Sani ya fito Tuwita ya na cewa: “A nemawa tubabbun ‘Yan ta’addan Boko Haram da aka dawo da su cikin al’umma sana’ar yi ko kuma a ba su jari.”

A jiya Laraba, 5 ga Wata Fubairun 2020, Sanata Sani ya kara da rubuta cewa: “Domin a tabbatar da tubansu (ya zama ba su yi tuban mazuru ba)”.

A yau Alhamis kuma an ji tsohon ‘Dan majalisar ya na cewa mafi yawan wadanda ‘Yan ta’addan Boko Haram su ka hallaka a Najeriya Musulmai ne.

Sai dai duk da wannan ta’adi, ‘Dan siyasar ya nuna cewa wannan muguwar kungiya ta na da wata tsana ta musamman da ta yi wa duka Kiristoci.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel