Shari'ar Zazkzaky: An tsananta tsaro a Kaduna
A yau Alhamis ne aka tsaurara tsaro a cikin garin Kaduna sakamakon ci gaba da shari'ar shugaban Islamic Movement of Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim El Zakzaky da matarsa, Zeenat.
Za a ci gaba da sauraron shari'ar shugaban kungiyar Musulmai mabiya akidar shi'a din ne a babbar kotun jihar Kaduna.
Jami'an tsaro sun mamaye duk wasu manyan titunan da ke kaiwa zuwa ginin babbar kotun jihar Kaduna, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.
Hakazalika, an tsananta tsaro a farfajiyar kotun don gujewa karantsaye ga doka ballantana kuma a kai ga zanga-zanga daga mabiyan akidar shi'an.
El-Zakzaky da matarsa suna fuskantar tuhuma a kan laifuka takwas da gwamnatin jihar Kaduna ke zarginsa da su, wadansa suka hada da kisan kai, taro ba bisa doka ba da kuma hana zaman lafiya ga mutane da sauransu.
DUBA WANNAN: Tsaro: Hotunan sabbin jiragen yaki da kasar Rasha ta kera wa Najeriya
A wancan zaman kotun da ya gabata na ranar 5 ga watan Disamba 2019, babban alkalin kotun, Mai shari'a Gideon Kurada ya ba hukumar jami'an tsaron fararen kaya umarni a kan su mayar da shugaban IMN din da matarsa zuwa gidan gyaran hali na jihar Kaduna, don ba lauyoyinsu damar samunsu.
Mai shari'a Kurada ya bada umarnin nan ne kafin a fara sauraron bukatar belin shugaban IMN din kamar yaddda Haruna Magashi ya bukata. Watanni takwas bayan da aka dage shari'ar a ranar 26 ga watan Maris na 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng