Boko Haram na gab da ganin bayan mu baki daya - Mutanen garin Chibok

Boko Haram na gab da ganin bayan mu baki daya - Mutanen garin Chibok

- Shugaban kungiyar jama’a mazauna garin Chibok da ke jihar Borno ya koka da rashin cika alkawarin da gwamnatin shugaba Buhari tayi musu

-Shugaban mai suna Dauda Iliya ya ce Shugaba Buhari yayi musu jajen sace ‘ya’yansu da aka yi tare da alkwarin za a kafa kwamitin nemo su

- Mazauna garin Chibok din sun yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayyar a kan ta kawo musu dauki kafin a wayi gari a ga ba kowa a garin

Shugaban kungiyar mazauna garin Chibok da ke jihar Borno mai suna Dauda Iliya wanda aka fi sani da ‘Kibaku’ ya bayyana cewa, a ranar 14 ga watan Janairu na 2016 ne shugaban kasa yayi wa iyayen ‘yan matan da aka sace jaje. Ya kara da cewa Shugaba Buhari yayi wa iyayen jaje tare da alkawarin cewa gwamnati za ta kafa kwamiti domin tsara hanyoyin da za a bi don ceto sauran ‘ya’yansu.

Iliya ya ce shekaru hudu sun wuce amma shugaba Buhari bai cika alkawarin da ya daukar musu ba.

Boko Haram na gab da ganin bayan mu baki daya - Mutanen garin Chibok
Boko Haram na gab da ganin bayan mu baki daya - Mutanen garin Chibok
Asali: Facebook

Ya ce a yanzu haka babu wanda ya san inda yaran su suke ko irin hobbasan da gwamnati ke yi don ceto su tun a wancan lokacin zuwa yanzu, kamar yadda jaridar Premium Times Hausa ta ruwaito.

Duk da ikirarin gwamnati na cewa ta gama da Boko Haram, harin da ake kai wa yankin Arewa maso gabas din na karyata wannan ikirarin.

Ko a jajiberin Kirsimetin 2019, mayakan Boko Haram sun kai hari wani kauye mai suna Kwarangilum da ke kusa da Chibok. Sun yi garkuwa da mutane biyar kuma sun kona gidaje tare da yin awon gaba da dabbobin mutane.

KU KARANTA: Tashin hankali: Ladani ya bawa makwabcinsa zakami ya sha ya mutu

Kwanaki biyar bayan wannan harin, mayakan sun kara fadawa kauyen Mandaragrau inda suka yi garkuwa da ‘yan garin Chibok din har 17.

Mazauna garin sun yi kira da babbar murya ga gwamnati a kan ta gaggauta daukar mataki don wata rana za a wayi gari a ga babu kowa a garin sakamakon dauki dai-dai da ake musu.

Idan ba a manta ba, a ranar 15 ga watan Afirilu na 2014 ne mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da daliban makarantar sakandiren ‘yan mata da ke Chibok har su 276.

164 daga cikin daliban sun koma ga iyayensu sai dai sauran har yanzu ba amo balle labari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel