Majalisar Kano ta zabi sabon shugaban masu rinjaye

Majalisar Kano ta zabi sabon shugaban masu rinjaye

A ranar Laraba ne majalisa dokokin jihar Kano ta tsige shugaban masu rinjaye, Alhaji Labaran Abdul Madari, tare da maye gurbinsa da mataimakinsa, Alhaji Kabiru Hassan Dashi.

An tsige Abdul Madari, dan jam'iyyar APC da ke wakiltar mazabar Warawa, biyo bayan bukatar da wani mamba dan jam'iyyar APC a majalisar, Alhaji Muhammad Uba Gurjiya, mai wakiltar karamar hukumar Bunkure, ya gabatar.

Bukatar dan majalisar ya samu goyon bayan Honarabul Ali Ibrahim Shanono, mai wakiltar mazabar Bagwai/Shanono.

Rahotanni sun bayyana cewa an rantsar da Uba Gurjiya ranar Talata yayin zaman majalisar da shugabanta, Abdulazeez Garba Gafasa, ya jagoranra. An rantsar da shi ne biyo bayan nasarar da ya samu a zaben maye gurbi da aka kammala kwanakin baya bayan nan.

A cewarsa, majalisar ta yanke shawarar cire shugaban masu rinjayen ne biyo bayan amincewar mambobin 23 daga cikin 28 da jam'iyyar APC ke dasu a cikin jimillar mambobi 40 da majalisar jihar keda su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel