Da dumi dumi: Annobar zazzabin Lassa ta kashe mutane 2 a jahar Katsina

Da dumi dumi: Annobar zazzabin Lassa ta kashe mutane 2 a jahar Katsina

Annobar cutar zazzabin Lassa ta bulla a jahar Katsina, inda ta kama mutane biyu, sa’annan ta kashe mutum 1 daga cikinsu, kamar yadda sakataren hukumar kiwon lafiya ta jahar Katsina ya tabbatar.

Shugaban hukumar, Dakta Shamsuddeen Yahaya ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Laraba, 5 ga watan Feburairu, inda yace an samu bullar jahar Katsina a kan mutane 7, sa’annan gwaji ya nuna mutane hudu basu da shi.

KU KARANTA: Kotu ta bada umarnin a kashe magidanci ta hanyar rataya saboda ya kashe matarsa

Jaridar Katsina Post ta ruwaito shi yana cewa akwai wasu sakamakon gwaji guda biyu da suka tabbatar da zazzabin akan mutane biyu, amma ba’a riga an maido musu su ba, sai kuma wani guda daya da aka tsumayin samun sakamakon sa.

Daga cikin wadanda aka samu da cutar akwai wata mata mai dauke da juna biyu dan wata uku dake zaune a kauyen Kwarin Yashe na karamar hukumar Kusada wanda ta rasu a daren Laraba, sai kuma wata mata guda da ake dubata a babban asibitin Kankia.

A wani labarin kuma, wani likita daga babban asibitin Kankia ya tabbatar da cewa an samu mutane hudu mata dauke da cutar zazzabin Lassa, kuma cutar ta harbesu ne bayan wata tafiya da suka yi zuwa jahar Bauchi.

Daga cikin matan hudu, guda ta mutu tun kafin a garzaya da ita asibiti, yayin guda ta warware daga zazzabin, sai dai daga cikin guda biyu da aka mikasu zuwa asibitin daya ta sake mutuwa, amma daya tana samun sauki.

A cewar majiyar Legit.ng, har zuwa lokacin tattara wannan rahoto gawar matar na nan a asibitin Kankia, kuma wanda take samun saukin ma tana nan a asibitin. da aka tambayeshi ta yaya suke kundunmbalan kulawa da marasa lafiyan, sai yace suna dai tabbatar da sun yi takatsantsan sosai.

A wani labarin kuma, wata babbar kotun tarayya dake zamanta a garin Jabi ta yanke hukuncin kisa a kan wani matashi dan shekara 38, Eric Chigbor, ta hanyar rataya bayan ta kama shi da laifin kisan kai, inda ya kashe matarsa.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya,NAN, ta ruwaito rundunar Yansanda ta tuhumi Eric da aikata laifin kisan kai, inda rundunar ta ce laifin ya saba ma sashi na 220 na kundin hukunta manyan laifuka, kuma kundin ya tanadi hukunci ga duk mai laifin a sashi na 221.

Majiyarmu ta ruwaito a ranar 3 ga watan Feburairun 2015 ne Eric ya garzaya da gawar Jessica zuwa asibiti a garin Bwari inda ya shaida ma masu kula da gawa cewa Jessica ta kashe kanta ta hanyar kurbar fiya fiya, amma makwabtansa suka karyata shi, inda suka ce dukanta yake yi, har ya kulle kofa don kada a bata agaji.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel