Labari mai dadi: Amurka ta bawa Najeriya tallafin dala miliyan 40 don yaki da ta'addanci

Labari mai dadi: Amurka ta bawa Najeriya tallafin dala miliyan 40 don yaki da ta'addanci

- Kasar Amurka ta sanar da ba wa Najeriya tallafin kudi har dala miliyan 40 don yakar ta'addanci a kasar nan

- Wannan ya biyo baya ne kwanaki hudu bayan Amurka ta haramtawa 'yan Najeriya Visa din shiga kasar

- A taron da sakataren kasar da ministan harkokin waje na Najeriya suka yi, sun tattauna kan tsaro, kasuwanci da zuba hannayen jari

Kasar Amurka ta sanar da cewa za ta ba Najeriya tallafin dala miliyan 40 a matsayin taimako ga jama'ar kasar da ta'addancin 'yan Boko Haram ya shafa.

Mike Pompeo, sakataren kasar ne ya sanar da hakan a ranar Talata a birnin Washington DC a yayin wani taro tare da ministan harkokin waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, in ji jaridar The Cable.

Wannan ci gaban ya biyo baya ne cikin kwanaki hudu da kasar Amurka ta haramtawa 'yan Najeriya Visa.

Kasa da sa'o'i 24 bayan haramta Visa din, kasar Amurka ta gayyaci Onyeama a kan su tattauna tare da wakilanta a birnin Washington DC don tattauna kasuwanci, tsaro da mulki na gari.

A yayin jawabi a taron US-Nigeria Binational Commission, wanda sashen kasar ya bada masauki, Pompeo ya ce Amurka ta gano cewa yaki da ta'addancin na da matukar wuya. Ya kara wa gwamnatin Najeriya karfin guiwa a kan ta dage don kare rayukan farar hula da suka hada da bangarorin addinai da masu bada taimako.

KU KARANTA: Mata sun fi kowa iya tattali, dan haka su ya kamata a tallafawa - Amaechi

"Ministan Najeriya da ni mun kammala tattaunawa a kan yadda tattalin arziki zai habaka da tsaro a tsakanin kasashen. Wannan dole ne mu mayar da hankali don Najeriya ce kasa mai babban tattalin arziki a Afirka," Pompeo ya ce.

"Ni da ministan mun tattauna a kan tsaro wanda ya danganci ta'addancin Boko Haram da ISIS. Mun san akwai wuya amma ina ba gwamnatin Najeriya kwarin guiwa da ta kokarta wajen kare rayukan farar hula.

"Don tallafawa a wannan bangaren, ina farin cikin sanar da cewa Amurka za ta tallafawa Najeriya da $40 miliyan." Cewar Pompeo.

A bangaren Onyeama, ya mika godiya ga Amurka a kan tallafin da ta ba Najeriya. Ya ce kasar nan shirye take don yin kasuwanci da Amurka tare da daukar hankalin masu zuba hannayen jari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel