Mata sun fi kowa iya tattali, dan haka su ya kamata a tallafawa - Amaechi

Mata sun fi kowa iya tattali, dan haka su ya kamata a tallafawa - Amaechi

- Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce kamata yayi a fi mayar da hankali wajen tallafawa mata saboda sun fi iya tattali

- Amaechi ya mika godiyar shi ga ma'aikatar kwadago da aikin yi ta kasa ta yadda za ta ba mutanen jihar Ribas 5000 bashi babu ruwa

- Festus Keyamo ya ce gwamnatin shugaba Buhari ta matukar damuwa da walwalar talaka tare da burin tsamo su daga talauci

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce kamata yayi a tallafawa mata sosai saboda sun iya tattali.

Amaechi ya sanar da hakan ne a wani shirin bada tallafi ga mata da matasa wanda ofishin karamin ministan kwadago da aikin yi ya bada, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

Ya mika godiyar shi ba shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kokarin da yayi na habakawa tare da tallafawa jama'ar jihar Ribas da bashi don kasuwanci da aiyukan dogaro da kai.

"Mutane dubu biyar za a ba bashi babu ruwa. Daga N100,000 zuwa N5 miliyan kuma za a ba maza da mata ne. A cikin 5000 din za a ba mata 3000 ne saboda sun iya tattali," ya ce.

"Ban ce kyauta ba, na ce bashi ne babu ruwa. Yana nufin zaku biya. Sai mun ga tsarin kasuwancinku da yadda zai tafi. Ba zamu karba ruwa ba saboda bamu son takura muku.

"Muna godiya ga karamin ministan da kuma shugaba Buhari. NDE za ta horar da mutane 30 a kowacce karamar hukumar ta jihar kuma za a samar musu da aikin da suka koya. Gwamnatin tarayya za ta dinga biyansu duk wata."

KU KARANTA: Dan gudun hijira mai shekaru 15 ya daure kanshi a kasan babbar mota domin ta shiga dashi kasar Birtaniya

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, ya ce shugaban kasa ya damu da walwalar talakawa.

"Wannan na daya daga cikin ire-iren aiyukan da shugaban kasa ke umartarmu da mu shirya don cire miliyoyin mutane daga talauci a kowacce shekara," ya ce.

"A duk lokutan da aka je taro kuma aka gabatar da wani tsari, tambayar farko da shugaban kasa yake yi itace aiyuka nawa tsarin zai samarwa 'yan Najeriya? Wannan ce gwamnati ta farko bayan shekaru masu yawa da ke damuwa da jama'arta. Saboda hakan ne shugaban kasar ya damu da talakawa." Keyamo ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel