Katsina: Matar aure mai shekaru 17 da caka wa mijinta wuka ya mutu saboda cajar waya

Katsina: Matar aure mai shekaru 17 da caka wa mijinta wuka ya mutu saboda cajar waya

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina a ranar Talata sun kama wata matar aure mai shekaru 17 mai suna Rabi Rabi'u. An zargeta da sokawa mijinta mai suna Shamsu Salisu wuka mai shekaru 25 a kauyen Almakiyayi da ke karamar hukumar Malumfashi ta jihar.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya sanar da manema labarai cewa DPO din Malumfashi ya amsa kira gaggawa da aka yi masa a kan aukuwar lamarin.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Rabi ta soki mijinta a waurare da dama a jikinsa wanda ya hada da cikin shi yayin da yake bacci. Hakan ne kuwa yayi ajalin mijin nata, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Katsina: Matar aure mai shekaru 17 da caka wa mijinta wuka ya mutu saboda cajar waya
Katsina: Matar aure mai shekaru 17 da caka wa mijinta wuka ya mutu saboda cajar waya
Asali: Twitter

Ya ce "Sakamakon raunikan da ya samu, 'yan sandan sun gaggauta mika shi babban asibitin Malumfashi inda aka tabbatar da cewa ya rasu."

"A yayin binciken 'yan sandan, sun samo wuka mai kaifi tare da zanin gadon da yayi kaca-kaca da jini. Har a yanzu dai ana ci gaba da bincike". Ya kara da cewa.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun kama mijin da ya garkame matansa biyu a gida yana bautar da su a Katsina

A wani ci gaba makamancin hakan, rundunar 'yan sandan ta kama wani mutum mai shekaru 30 mai suna Sama'ila Musa na kauyen Yan-Nabayye da ke karamar hukumar Rimi. An zargesa ne da daurewa tare da bautar da matansa biyu; Fatima da Hadiza. A hakan kuma yake saduwa dasu.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah ya sanarwa manema labarai a ranar Talata a garin Katsina, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce Musa na zaune ne a kauyen Yan-Nabayye da ke karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina. Isah ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan bibiyarsa da aka dinga yi.

"A ranar 23 Janairu, 2020 wajen karfe uku da rabi na yamma, rundunar 'yan sandan jihar tayi nasarar kama wani Samaila Musa mai shekaru 30 daga kauyen Yan-Nabayye a karamar hukumar Rimi ta jihar. Ana zarginsa da zama jigo a wata kungiyar asiri a jihar," ya ce

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel