Dan gudun hijira mai shekaru 15 ya daure kanshi a kasan babbar mota domin ta shiga dashi kasar Birtaniya

Dan gudun hijira mai shekaru 15 ya daure kanshi a kasan babbar mota domin ta shiga dashi kasar Birtaniya

- Wani yaro dan gudun hijira ya makale a wata motar daukar kaya mai lambar birtaniya don tseratar da rayuwarshi bayan an kashe iyayenshi

- Direban motar mai suna Kyle ya ce sai da yayi tafiyar mil 25 sannan ya gane cewa akwai mutum a cikin kayan da ya debo

- Ya taimaka mishi da €100 kuma ya sauke shi a Hayes da ke Hillington a yammacin London inda ya samu sansanin 'yan gudun hijirah

Wani yaro dan gudun hijirah ya makale a wata motar daukar kaya ta Birtaniya a kokarin shi na guduwa daga yakin da ya hargitsa Dafur.

Matukin motar ya ce bayan ya tsaya a wani otel da ke Tunnel Sous la Manche, kusa da iyakar Calais a ranar 14 ga watan Janairu a kan hanyar shi ta zuwa Paris, ya ce ya fara jin ihu a kusan nisan mil 20. Ya yi kamar bai ji ba inda ya ci gaba da tafiya don yayi tunanin kayan da ya dauko ne.

Direban dan asalin Birtaniya ya sanar da Metro cewa: "Bayan tafiyar mil 25 sai bugun da ihun suka ki karewa. Na fita don dubawa amma sai na ga matashin yaro yana rawar sanyi. Ya nemi ya gudu amma sai na sanar da shi ba zan cutar dashi ba."

Duk da yaron ya ce shekarun shi 18, direban ya ce ba zai wuce 15 ba dan asalin kasar Sudan din, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

KU KARANTA: Munashe Ncube: Matar aure da take zina da maza 16 a titi

Yaron dan gudun hijarar ya ce ya zauna a kasan motar ne na sa'o'i hudu bayan ya ga lambar UK ce a motar.

"Ya ce min an kashe iyayenshi kuma neman tsira da ranshi yasa ya biyo ni." Cewar direba Kyle wanda ya dau tsawon shekaru 12 yana tuki.

Daga baya matukin motar ya sauke Saudi a Calais tare da bashi €100 da kuma adireshin shi.

"Na ce ba zan iya tafiya da shi Ingila ba amma ina mishi fatan alkhairi." Cewar Kyle.

Bayan kwanaki, direban ya gano cewa Saudi na wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Hayes, Hillington da ke yammacin London.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel