Tashin hankali: Mutanen gari sun bugu sunyi mankas, bayan 'yan sanda sun kone mota guda ta tabar wiwi

Tashin hankali: Mutanen gari sun bugu sunyi mankas, bayan 'yan sanda sun kone mota guda ta tabar wiwi

- Mazauna yankin yammacin Jakarta da ke kasar Indonesia sun shiga halin dimuwa da buguwa wacce hayakin wiwi ya jawo musu

- Hakan ya biyo bayan kona wiwi da wasu miyagun kwayoyi da 'yan sandan yankin suka yi wadanda suka karba daga masu safara

- Mazauna yankin sun bayyana cewa sun yi fama da jiri, ciwon kai da hargitsewar tunani bayan shakar mugun hayakin

Ka kwatanta cewa kana zaune kana zaune a gida yayin tunanin wani abu mai amfani ko kuma mutum na shawagi a gari yayin nemo biredi kawai sai ya bugu. Za ta iya yuwuwa tare kake da 'ya'yanka sai hayakin wiwi ko wata muguwar kwaya ya hargitsa muku tunani.

'Yan sanda ne suka yi kuskuren bugar da jama'ar wani yanki ta hanyar kona wiwi mai nauyin tan 3.

'Yan sandan yankin yammacin Jakarta da ke kasar Indonesia ne suka bankawa wiwi mai tarin yawa wuta wanda yayi sanadiyyar buguwar mutanen yankin, kamar yadda jaridar Pulse ta ruwaito.

Tashin hankali: Mutanen gari sun bugu sunyi mankas, bayan 'yan sanda sun kone mota guda ta tabar wiwi
Tashin hankali: Mutanen gari sun bugu sunyi mankas, bayan 'yan sanda sun kone mota guda ta tabar wiwi
Asali: Facebook

Karin tashin hankali a yankin ya auku ne bayan da suka hada da kwayoyi 2563 tare da wata wiwi din wacce suka kwace daga masu safarar miyagun kwayoyi, in ji jaridar Rare.us.

KU KARANTA: Tsananin gajiya ta sanya doki mutuwa a tsakiyar titi, bayan an koma yin acaba da shi a Legas

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan sandan sun rufe hancinsu da bakunansu don kariya daga mummunan hayakin mai bugarwa, sun ki sanar da mazauna yankin don daukar matakan da suka dace kafin kone-konen.

Mazauna yankin sun yi korafin cewa sun yi fama da jiri, ciwon kai tare da hautsinewar tunani bayan sun shaki mugun hayakin.

Toh, duk da wannan kwabar ta 'yan sandan ta jawo wa mazauna yankin rashin jin dadi, akwai tabbacin cewa ranar ta fi ta sallah ga masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel