Tsananin gajiya ta sanya doki mutuwa a tsakiyar titi, bayan an koma yin acaba da shi a Legas
- Wani gajiyayyen doki ya fadi kasa warwas a tsakiyar titi bayan yayi aiki ya gaji a Legas
- Hakan ya biyo bayan kai da kawowa da yayi tayi bayan haramta aikin achaba da adaidaita sahu da gwamnatin jihar tayi
- Bayan haramta aikin achaba da adaidaita sahu da gwamnatin jihar tayi, wasu daga cikin mazauna yankin sun fara amfani da dawakai
Wani gajiyayyen doki ya fadi kasa warwas a tsakiyar titi bayan yayi aiki mai matukar wahala sakamakon hana achaba da adaidaita sahu yawo a Legas.
Bayan an haramta achaba da adaidaita sahun yawo a titunan Legas, an ga dawakai na ta shawagi da mutane a titunan. Ana yawo ne da dawakan don kai da kawo mutane a jihar, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Asali: Facebook
Wani bidiyon doki da ya fadi baya ko motsi a tsakar titi a kan babbar hanya a Legas din ya jawo cece-kuce bayan an wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita. Wasu sun dinga cewa dama can wannan aikin ba na doki bane don bashi da kayan aiki kamar karfen nasara.
KU KARANTA: Dubu 600 nake samu duk wata da sana'ar acaba - Cewar wata mata da take acaba a Legas
A cikin makon nan ne gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya haramta achaba da adaidaita sahu a wasu lunguna da sakuna na jihar Legas din.
Wannan dokar ta jawo tashin-tashina a fadin jihar don wasu 'yan achaba da matukan adaidaita din har zanga-zanga suka yi. Sun nuna damuwarsu ta yadda gwamnatin jihar ke yunkurin datse musu hanyar cin abinci.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng