Gwamnan Ondo ya ziyarci Villa, ya nemi Buhari ya samar da dokar halasta tabar wiwi

Gwamnan Ondo ya ziyarci Villa, ya nemi Buhari ya samar da dokar halasta tabar wiwi

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya yi kira ga gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta kirkiro dokoki da zasu halasta ta’ammali da tabar wiwi a Najeriya.

Gwamna Rotimi ya bayyana haka ne yayin ziyarar daya kai fadar gwamnatin Najeriya, Aso Rock Villa a ranar Talata, 4 ga watan Feburairu inda ya yi ganawar sirri da shugaban kasa Buhari a ofishinsa, inda yace jaharsa za ta zuba hannun jari don hada magungunan kwayoyi daga tabar wiwi.

KU KARANTA: Hukumar ICPC ta fitar da bayani game da daukan mutane 220 aiki cikin dubu 376 da suka nema

Gwamnan Ondo ya ziyarci Villa, ya nemi Buhari ya samar da dokar halasta tabar wiwi
Gwamnan Ondo ya ziyarci Villa, ya nemi Buhari ya samar da dokar halasta tabar wiwi
Asali: Facebook

Da yake zantawa da manema labaru bayan kammala ganawarsa da Buhari, Gwamnan yace makasudin ziyarar daya kai ma shugaba Buhari shi ne domin ya gayyace shi zuwa garin Akure don ya kaddamar da gadar sama a Ore daya gina a kan kudi naira biliyan 5, da kuma cibiyar masana’antu na jahar Ondo.

Gwamnan ya kara da cewa Buhari zai kaddamar da wadannan ayyuka ne don taya shi murnar cika shekaru uku a kujerar gwamnan. Haka zalika gwamnan ya tabbatar da cewa tuni ya fara biyan N33,000 a matsayin karancin albashi ga ma’aikata.

“Ma’aikatan jahar Ondo sun fi kowa jin dadi a kasar nan saboda suna samun albshinsu a kan lokaci, kuma tuni muka fara aiwatar da sabon tsarin karancin albashi. Dalilin da yasa ban goyi bayan kungiyar tsaro ta Amotekun ba shi ne saboda bana bukatar wannan kafin jama’a su sake zabana a karo na biyu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Hukumar yaki da rashawa da dangoginsu, ICPC, ta fitar da wani sanarwar dake dauke da sabbin bayanai game da aikin da ta sanar da za ta dauka a cikin sabuwar shekarar 2020, wanda a kwanakin baya ta sanar ma yan Najeriya masu sha’awa su nema.

Hukumar ta bayyana cewa biyo bayan kulle amsan takardun masu sha’awar aikin, ta kidaya mutane 376,631 daidai da suka nuna sha’awarsu na yin aiki a cikinta, sai dai hukumar ta kara da cewa gurabe 220 take dasu kacal.

ICPC ta bayyana haka ne a shafin ta na Facebook, inda tace akwai ire iren mutanen da take bukatar dauka daga cikin wadanda suka nemi ayyukan, daga cikinsu akwai wadanda suka karanci kididdigar kudi, sharia, tsimi da tanadi, kimiyyar kwamfuta, lissafi, jarida, zane, da sauran manyan kwasa kwasai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel