Bai taba addinin Musulunci ba ko na sa'a daya - Mahaifin Nathaniel Samuel

Bai taba addinin Musulunci ba ko na sa'a daya - Mahaifin Nathaniel Samuel

Mahaifin Nathaniel Samuel, matashin da aka damke yana kokarin tayar da Bam a cocin Living Faith Church dake Kaduna, Mr Samuel Ezekiel, ya tabbatar da cewa 'dansa Kirista ne, ba Musulmi ba kamar yadda ake yadawa. Daily Trust ta ruwaito.

Zaku tuna cewa ana ta cece-kuce kan addini da sunan matashin musamman yayinda kungiyar mabiya addinin Kirista CAN suke kokarin nisantash da addininsu.

A ziyarar da DT ta kai gidan mahaifinsa dake kauyen Marabar Demishi, harin Maraban Rido, a karamar hukumar Chikun na jihar, an tattauna da mahaifinsa, Samuel Ezekiel da shugaban kungiyar CAN, Joseph Hayab.

Mahaifin ne dan asalin jihar Bauchi ne kuma kabilar Jarawa kuma mahaifyarsa yar jihar Nasarawa ce.

Ya bayyana cewa an haifi Nathaniel Samuel a shekarar 1991.

Mahaifin ya bayyanawa Daily Trust cewa 'dansa mabiyi addinin Kirista ne kuma bai taba addinin Musulunci ba.

Yayind aaka tambayesa shin sunan 'dansa Mohammed Sani kamar yadda ake radawa, yace: "A'a, bai taba addinin Musulunci ba ko na kwana daya."

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta bayyana bayanai a kan mutumin da aka kama da bam a cocin Living Faith da ke Sabon Tasha a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar.

An bayyana sunansa da Nathaniel Samuel, mutum mai matsakaicin shekaru wanda 'yan sandan suka mika ga sashin binciken manyan laifuka don amsa tambayoyi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, hankula sun tashi ne bayan da wani mamban cocin ya ankarar da jami'an tsaro cewa ya ga wani mutum na dasa wani abu mai fashewa a yayin da ake bauta.

A nan ne aka tunkaresa tare da cafke shi kafin daga bisani a cire bam din a sannu.

An gano cewa, ba wannan ne karo na farko da wanda ake zargin ya fara zuwa cocin ba. Ya je cocin a makon da ya gabata amma sai aka kore shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, DSP Yakubu Sabo ya bayyanawa gidan talabijin din Channels cewa za a binciki Samuel a kan dalilin da yasa ya shiga wajen bautar da abu mai fashewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel