'Yan sanda sun kama mijin da ya garkame matansa biyu a gida yana bautar da su a Katsina

'Yan sanda sun kama mijin da ya garkame matansa biyu a gida yana bautar da su a Katsina

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta kama wani mutum da take zargi da zama dan kungiyar asiri mai suna Sama'ila Musa. Mutumin mai shekaru 30 ya shiga hannu ne bayan an kama shi da laifin daurewa tare da bautar da matansa biyu na tsawo lokaci.

Kakakin rundunar 'yan sandan, SP Gambo Isah ya sanarwa manema labarai a ranar Talata a garin Katsina, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Ya ce Musa na zaune ne a kauyen Yan-Nabayye da ke karamar hukumar Rimi ta jihar Katsina.

Isah ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan bibiyarsa da aka dinga yi.

"A ranar 23 Janairu, 2020 wajen karfe uku da rabi na yamma, rundunar 'yan sandan jihar tayi nasarar kama wani Samaila Musa mai shekaru 30 daga kauyen Yan-Nabayye a karamar hukumar Rimi ta jihar. Ana zarginsa da zama jigo a wata kungiyar asiri a jihar," ya ce.

DUBA WANNAN: Turai Yar'adua ta ziyarci Aisha Buhari a fadar shugaban kasa (Hotuna)

"Rundunar 'yan sandan da suka samu jagorancin DPO din yankin Rimi, sun gano gidan wanda aka zargi. Kuma ya daure matansa biyu tare da saka su a mari a daki daya. A yayin bincike, 'yan sanda sun gano tabban duka da ke jikin matan. A nan suke fitsari da bayan gida. An kuma aske gashin kansu don asiri da shi." Kakakin ya sanar.

"Ya daka yaji wanda yake saka musu a gabansu da idanunsu yayin da suke jinin al'ada. Wanda ake zargin na sa su shan ruwan maniyyi bayan ya sadu dasu." ya kara da cewa.

Isah ya kara da cewa 'yan sandan sun kama wani Sulaiman Salisu mai shekaru 35 daga kauyen Yar-Tsamiya wanda suke hada kai wajen aikata laifin.

A yayin da aka tattauna da wanda ake zargin da manema labarai, ya ce ya dauresu ne saboda suna shan miyagun kwayoyin kuma baya dukansu.

Amma kuma matan sun tabbatar da abinda 'yan sandan suka fara sanar da manema labarai.

An daure daya daga cikin matan na makonni 10 ne inda dayar kuwa aka daureta na watanni goma.

Sun kara da bayyana cewa suna rayuwarsu su kadai ne don babu mai zuwa ziyartarsu

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel