Allah ya yi wa jakadan Saudiyya a Najeriya rasuwa

Allah ya yi wa jakadan Saudiyya a Najeriya rasuwa

Rahotannin da ke samun jaridar Daily Nigerian na bayyana cewa jakaden kasar Saudi Arabia a Najeriya, Adnan Bostaji ya rasu a yau. Duk da ba a fitar da rahoton daga ofishin jakadancin ba, jaridar Daily Nigerian ta gano cewa jakaden ya rasu ne a asibitin kasa da ke Abuja bayan rashin lafiyar da yayi fama da ita.

"Za a mayar da gawarsa kasar Saudi Arabia don jana'izarsa da birnesa," in ji wata majiya daga ofishin jakadancin.

A yayin martani a kan mutuwar, shugaban hukumar hajji ta kasa, NAHCON, Abdullahi Mukhtar ya nuna damuwarsa. Ya ce mamacin na daya daga cikinmu jakadun da suka zo Najeriya masu matukar kwazo.

Mukhtar ya kara da cewa mutuwar Bostaji babban rashi ne ga al'ummar musulmi baki daya.

An haifa Bostaji a birnin Riyadh a shekarar 1966. Ya samu digirinsa na farko daga jami'ar Sarki Abdul Aziz dake Jiddah a 1985. Ya samu shaidar dufuloma a fannin dufulomasiyya a 1988.

Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa jakadan Saudiyya a Najeriya rasuwa
Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa jakadan Saudiyya a Najeriya rasuwa
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An gano ma'aikatan bogi 60,000 da tsarin IPPIS - Pantami

Ya fara aiki a ma'aikatar harkokin waje ta Saudi Arabia. Daga bisani an zabe sa a matsayin mataimakon jakaden Saudi a Tehran daga 1991 zuwa 1998.

Bostaji yayi aiki a Gulf Cooperation Council a ma'aikatar harkokin waje a 1998 zuwa 2000.

A 2000 an zabesa a matsayin shugaban ofishin jakadancin Saudi Arabia a Denmark har zuwa 2003.

Yayi aiki a matsayin shugaban lamurran tattalin arziki a ofishin jakadancin Saudi Arabia da ke London daga 2003 zuwa 2005. Ya koma ofishin ma'aikatar harkokin waje a Makka a matsayin darakta daga 2003 zuwa 2016.

Kafin a nada shi a matsayin jakadan Saudi Arabia a Najeriya, Bostaji ya rike matsayin mataimakin jakaden kasar Saudi Arabia a Berlin a 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel