Buhari ya aika wa Nanono takardar neman ya kare kansa a kan wata harkallar takin noma

Buhari ya aika wa Nanono takardar neman ya kare kansa a kan wata harkallar takin noma

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika takardar neman karin bayani ga ministan aikin noma, Sabo Nanono, a kan amincewa wasu kamfanoni da yayi kan su shigo da takin gona. Hakan kuwa ya ci karo da umarnin shugaban kasa Buhari na sarrafa taki a cikin gida Najeriya.

Jaridar ThisDay ta gano cewa ministan ya ba wasu masu shigo da taki lasisin ne don a hadiye gibin rashin takin da ake fama da shi a kasar nan.

An gano cewa abinda ministan yayi, yayi karantsaye ga dokar da shugaban kasa ya bada a shekaru uku da suka gabata don tabbatar da ana samar da taki a gida Najeriya.

Takardar neman karin bayani ta shugaban kasan ta samu sa hannun shugaban ma'aikatan fadar, Abba Kyari, wacce ke bukatar bayani a kan dalilin take dokar shugaban kasar.

Buhari ya aika wa Nanono takardar neman ya kare kansa a kan wata harkallar takin noma
Buhari ya aika wa Nanono takardar neman ya kare kansa a kan wata harkallar takin noma
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An saki muhimman bayanai a kan Samuel, matashin da ya yi yunkurin tayar da bam a Cocin Kaduna

An gano cewa takardar neman karin bayanin ta biyo bayan zanga-zangar da wasu masu samar da takin a cikin gida suka yi har suka sanar da fadar shugaban kasar abinda ministan yayi.

Fadar shugaban kasar ta bayyana damuwarta ta yadda abinda ministan yayi ya zamo barazana ga kamfanoni 28 wanda a ciki had da na Dangote mai tasowa a yanzu, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Idan zamu tuna, Kasashen Najeriya da Morocco sun sa hannu kan wata yarjejeniya a watan Disamba 2016 don taimakawa manoma farfado da kamfanonin taki ta hanyar samarwa da Najeriya sinadarin Phosphate.

Takardar yarjejeniyar wacce aka saka hannu a 2018 yayin da Buhari ya ziyarci Morocco, ta taimaka wajen farfado da kamfanoni 28 da suke daina aiki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng