Dalibar da aka kora a makaranta ta mallaki kamfanin biliyan 2 bayan fara sana'a da dubu 164

Dalibar da aka kora a makaranta ta mallaki kamfanin biliyan 2 bayan fara sana'a da dubu 164

- Alex Head ta zama ‘yar kasuwa mai matukar nasara bayan da aka koreta daga makaranta a lokacin da take da shekaru 15 a duniya

- Tana da shekaru 15, Alex ta bar makaranta don fada da tayi a kan abinci wanda hakan yasa ta koma koyon girke-girke

- Matar mai shekaru 34 ta ce ta bude wajen siyar da abinci ne ta yanar gizo wanda a halin yanzu arzikinta ya kai N1,883,639,200

Head ta bayyana cewa kora daga makaranta ba yana nufin ba zaka samu nasara bane a rayuwa. Alex tayi nasarar kafa kasuwancinta bayan da aka koreta daga makaranta.

Jaridar The Sun UK ta ruwaito yadda aka kori Alex Head daga makaranta a lokacin da take da shekaru 15 a duniya saboda fadan da tayi a kan abinci.

Ta kafa wajen siyar da abinci na kanta da kimanin N164, 760.85 a kusan shekaru tara da suka gabata. A duk shekara kuwa Alex na samun ribar da ta kai ta ninkin kudin jarinta.

Dalibar da aka kora a makaranta ta mallaki kamfanin biliyan 2 bayan fara sana'a da dubu 164
Dalibar da aka kora a makaranta ta mallaki kamfanin biliyan 2 bayan fara sana'a da dubu 164
Asali: UGC

Ta fara siyar da abincin ta yanar gizo a yayin da ta fara amfani da na’ura mai kwakwalwar kawarta bayan da aka koreta daga makaranta. Matar mai shekaru 34 ta fara daga siyar da abincin rana ne daga gida. Tana kaiwa abokan aikin mahaifinta abincin ne har ofishinsu.

KU KARANTA: Tashin hankali: An kama mutum 3 da suka yiwa dokuna, shanu, akuyoyi da karnuka fyade

Ta kokarta inda tayi jarabawar kammala sakandire don samun ci gaba da koyan girke-girkenta a wata makaranta mai suna Ballymaloe wacce ke kasar Ireland. Tana shekaru 18 ta koma jami’ar Oxford inda ta karanci karamci.

A halin yanzu Alex ta zama hamshakiyar mai arziki ta wannan kasuwanciin da ta fara. Arzikin Alex ya kai pam miliyan hudu wanda yayi dai-dai da N1,883,639,200.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel