Karin albashi: Kungiyar kwadago ta umarci ma’aikatan gwamnati su fara yajin aikin dindindin

Karin albashi: Kungiyar kwadago ta umarci ma’aikatan gwamnati su fara yajin aikin dindindin

Hadaddiyar kungiyar kwadagon Najeriya reshen jahar Neja ta umarci y’ay’anta da su zauna a gida a wani mataki na fara yajin aikin sai baba ta ji saboda gazawar gwamnatin jahar wajen biyan karancin albashin N30,000 ga ma’aikatan.

Daily Trust ta ruwaito shuwagabannin kungiyar ne suka fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu yayin da suka gana da manema labaru a garin Minna na jahar Neja, inda suka yi kira kafatanin ma’aikatan jahar Neja da su shiga yajin aiki a kan wannan batu.

KU KARANTA: Tabarbarewar tsaro: Gwamnati za ta yi daukan sabbin Sojoji na gaggawa – Osinbajo

Kungiyoyin sun hada da kungiyar kwadago, NLC a karkashin jagorancin kwamared Yakubu Garba da shugaban kungiyar yan kasuwa TUC, kwamared Yunusa D Tanimu, inda suka gindaya sharadin janye yajin aikin da har sai gwamnati ta fara biyan sabon tsarin karancin albashi na N30,000.

A kwanakin baya ne kungiyar ta baiwa gwamnatin jahar wa’adin kwanaki 21 domin ta aiwatar da dokar sabon tsarin karancin albashin ta hanyar biyan ma’aikata kudadensu a matsayin cika yarjejeniyar da suka yi da ita.

Haka zalika sanarwar da ta fito daga bakin shuwagabannin biyu ta yi kira ga gwamnati ta tabbata ta fara biyan wannan kudi, kuma ta biya ma’aikata kudin hutunsu na shekarar 2019.

A wani labari kuma, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai shirin daukan sabbin zaratan Sojoji nan bada jimawa ba a kokarin gwamnatin Najeriya na kara adadin jami’an tsaro domin su kawar da matsalar tsaro a kasar.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu yayin da ya karbi bakoncin wasu Fastoci a karkashin kungiyar fastocin yankin Arewacin Najeriya masu rajin kawo zaman lafiya a yankin.

Osinbajo ya bayyana cewa: “Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen matsalar tsaro, muna tafiyar da tsaron nan yadda ya kamata, daga ciki har da aika Sojoji bakin daga domin yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

“Har ma a yanzu zamu kara daukan sabbin Sojoji a rundunar Sojan kasa, kuma zamu dauke su ne a tsarin gaggawa, kuma zamu sayi karin makamai da sauran kayan aiki. A zaman karshe da muka yi na majalisar tsaro mun tattauna yiwuwar kara yawan Sojoji.

“Mun tattauna yadda zamu hada kai da matasa jarumai yan sa kai da sauran yan banga, don haka muna aiki tukuru wajen tsaurara matakan tsaro, musamman yadda zamu yi amfani da na’ura wajen leken asiri a kasar.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel