Asiri ya tonu: Bature ya yi shiga irinta bakar fata yaje ya yi fashi a banki

Asiri ya tonu: Bature ya yi shiga irinta bakar fata yaje ya yi fashi a banki

- 'Yan sandan kasar Amurka da ke yankin Perryville na jihar Maryland na neman wani dan fashi da makami ido rufe

- Sun wallafa hoton shi amma fuskarshi dauke da bakin fenti wanda aka zarga yayi ne don basaja

- Mutumin na da tsayin taku biyar zuwa biyar da rabi kuma yana da shekaru ne tsakanin 20 zuwa 30 a duniya

Wani mutum da yayi wa banki fashi ya boye fuskar shi ta hanyar sanya bakar fuska a Amurka. A halin yanzu dai jami'an 'yan sandan kasar Amurka na neman shi ido rufe.

Sashen 'yan sandan yankin Perryville suna neman mutumin ne bayan da yayi wa bankin PNC wanda ke yankin arewa maso gabas din jihar Maryland fashi da makami, kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito.

Asiri ya tonu: Bature ya yi shiga irinta bakar fata yaje ya yi fashi a banki
Asiri ya tonu: Bature ya yi shiga irinta bakar fata yaje ya yi fashi a banki
Asali: Facebook

Jami'an tsaron sun bukaci jama'a da su taimaka musu wajen gano wanda ake zargin. Mutumin ya fente fuskar shi har ta koma baka don neman yadda zai boye kamannin shi.

Mutumin jar fata ne mai tsayin tsakanin taku biyar zuwa biyar da rabi. Yana da matsakaicin shekaru tsakanin 20 zuwa 30 a duniya.

KU KARANTA: Babu babban bala'i a rayuwa irin mutum ya tashi ya ga an haifeshi a Najeriya - Peter Obi

"Muna bukatar taimakon jama'a da su taya mu gano wannan mutumin da ke hoton nan," 'yan sandan yankin Perryville suka wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook.

"Ana zargin shi da fashi da makami a bankin PNC da ke yankin Perryville wanda aka yi a ranar 28 ga watan Janairu.

"Bature ne kuma namiji ne. Yana da tsawon taku biyar zuwa biyar da rabi kuma yana da shekaru tsakanin 20 zuwa 30."

'Yan sandan sun wallafa hoton dan fashin bankin tare da fuskar shi wacce ta sha fentin baki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel