Tabarbarewar tsaro: Gwamnati za ta yi daukan sabbin Sojoji na gaggawa – Osinbajo

Tabarbarewar tsaro: Gwamnati za ta yi daukan sabbin Sojoji na gaggawa – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai shirin daukan sabbin zaratan Sojoji nan bada jimawa ba a kokarin gwamnatin Najeriya na kara adadin jami’an tsaro domin su kawar da matsalar tsaro a kasar.

Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 3 ga watan Feburairu yayin da ya karbi bakoncin wasu Fastoci a karkashin kungiyar fastocin yankin Arewacin Najeriya masu rajin kawo zaman lafiya a yankin.

KU KARANTA: Gwamna El-Rufai ya kara karfafa tsaro a tashar jirgin kasa dake Rigasa Kaduna

Premium Times ta ruwaito Osinbajo ya bayyana cewa: “Muna yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo karshen matsalar tsaro, muna tafiyar da tsaron nan yadda ya kamata, daga ciki har da aika Sojoji bakin daga domin yaki da Boko Haram a yankin Arewa maso gabas.

“Har ma a yanzu zamu kara daukan sabbin Sojoji a rundunar Sojan kasa, kuma zamu dauke su ne a tsarin gaggawa, kuma zamu sayi karin makamai da sauran kayan aiki. A zaman karshe da muka yi na majalisar tsaro mun tattauna yiwuwar kara yawan Sojoji.

“Mun tattauna yadda zamu hada kai da matasa jarumai yan sa kai da sauran yan banga, don haka muna aiki tukuru wajen tsaurara matakan tsaro, musamman yadda zamu yi amfani da na’ura wajen leken asiri a kasar.” Inji shi.

Bugu da kari mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana ma fastocin cewa gwamnati na sane da matsalolin da ake samu a garuruwan Arewacin Najeriya, kuma a shirye suke su magance wadannan barazanar tsaro.

Daga karshe Osinbajo ya yi kira ga malaman addinin dasu kawo shawarwari da zasu iya taimaka wajen kawo karshen matsalar. Shi ma a nasa jawabi, shugaban kungiyar, Bishop Mbayo Japhet yace sun kai ziyarar ne don bayyana goyon bayansu ga gwamnatin shugaban kasa Buhari da Osinbajon kansa.

A wani labari kuma, Kungiyar Boko Haram dake biyayya ga kungiyar ta’addanci ta duniya, ISIS, watau ISWAP ta kashe wasu zaratan dakarun Sojin Najeriya guda uku tare da kwace motocin yaki guda biyu a wani hari da suka kai ma Sojoji a ranar Juma’a.

Mazauna garin Askira sun bayyana cewa yan ta’addan sun dira garin ne da tsakar daren Juma’a a cikin wasu motocin a kori kura guda biyu da suka daura ma bindigu tare da alburusai, inda suka yi ta fafatawa da Sojoji da matasa yan sa kai a garin.

Wani jami’in Soja da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Sojojinmu sun fatattaki yan Boko Haram, amma sun kashe mana Sojoji uku, kuma sun tafi da motocin yakinmu guda biyu, sai dai mu ma mun kashe musu mayaka da dama.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel