Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

Abinda Buhari ya fada wa Lawan da Gbajabiamila a kan tsaro yayin ganawarsu

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kebe tare da shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan, da takwaransa na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Babu wani bayani ko sanarwa dangane da abin da zasu tattauna gabanin ganawar tasu, wacce suka fara da misalin karfe 3:00 na rana.

A makaon jiya ne majalisa ta yi kira ga shugaba Buhari a kan ya sauya shugabannin rundunonin tsaro na kasa ko kuma ta tsige su saboda gazawarsu wajen kawo karshen kalubalen tsaro da kasa ke fama da shi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaban majalisar dattijai Ahmad Lawan da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Shugaban kasar ya gana da shugabannin majalisar kasar nan ne a ranar Litinin cikin fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

Da duminsa: Buhari ya saka labule da Ahmed Lawan da Gbajabiamila a fadarsa
Buhari yayin gana wa da Ahmed Lawan da Gbajabiamila a fadarsa
Asali: Twitter

A yayin bayani ga manema labaran gidan gwamnati jim kadan bayan kammala ganawarsu, Gbajabiamila ya ce shugabannin majalisar ne suka ziyarci shugaban kasa domin samun bayanai dalla-dalla a kan halin da kasar nan ke ciki ta fuskar tsaro.

DUBA WANNAN: Babbar magana: Wani miji ya like al'aurar matarsa da 'super glue' don kar ta ci amanarsa

Kamar yadda Gbajabiamila ya sanar, shugaban kasar ya nuna musu damuwarsa a kan halin rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

Kakakin majalisar ya bayyana cewa, zancen sauke shugabannin tsaron kasar nan na cikin abubuwan da suka tattauna.

Amma kuma, ya ce har yanzu dai ba a cimma matsaya ba don kuwa akwai mabanbantan ra'ayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng