Dokar hana Achaba: Rikici ya barke tsakanin yan babur da yan sanda a Legas, an kashe mutane 3
Wasu yan achaba da matukan Keke Napep da akafi sani da 'a daidaita sahu' sun gudanar da zanga-zanga a unguwar Ijora ta jihar Legas ranar Litinin kan dokar hana aikin babur da Keke Napep a jihar.
An samu labarin cewa an fara takaddama ne lokacin da yan sanda sukayi kokarin hana su zanga-zangar.
Yayinda suka kaddamar da zanga-zangar misalin karfe 8:21 na safe, yan babur da yan Keke Napep sun tare hanyoyi suna kona tayoyin mota.
Rahoton The Nation ya nuna cewa an bindige mutane uku a yanzu kuma matasa sun tare hanya.

Asali: Facebook

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng