Yan bindigan daji sun yi ma motar fasinja ruwan wuta a babbar hanyar Abuja – Lokoja

Yan bindigan daji sun yi ma motar fasinja ruwan wuta a babbar hanyar Abuja – Lokoja

Wasu gungun miyagu yan bindiga sanye da kayan Sojoji da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun bude ma wasu babbar motar Luxurious wuta a kan hanyar Abuja zuwa Lokoja inda suka ji ma mutane hudu rauni.

Daily Trust ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a gab da kauyen Gada-Biyu dake kan hanyar Abuja zuwa Lokoja a ranar Lahadi, 2 ga watan Feburairu, inda yan bindigan suka bude ma motar kamfanin Chisco wuta mai lamba AGL 11 XL.

KU KARANTA: Shuwagabannin PDP sun gudanar da zanga zanga a ofishin Amurka da Birtaniya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito direban babbar motar mai suna Madu Francis ya bayyana cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 5:47 na yamma a lokacin da yake gangarawa Gada-Biyu, kwatsam sai ganin wasu mutane sanye da kakin Sojojo sun fito daga cikin daji sun bude musu wuta da bindigu.

Madu ya kara da cewa adadin yan bindigan yah aura 30, don haka wutan da suka bude ma motar tare da fasinjojinta ya yi karfi sosai, wanda hakan yasa da dama daga cikinsu suka samu rauni a sanadiyyar harbe harben.

“Amma cikin ikon Allah sai tsugunna na cigaba da rike da motar, a sakamakon haka ne harsashi daya ya goge ni a kai, amma haka na cigaba da tuka motar har muka kai garin Abaji muka tsaya, daga nan aka garzaya da fasinjoji uku zuwa asibiti don samun kulawa.” Inji shi.

A wani labari kuma, Wasu manoma guda biyu sun gamu da ajalinsu a hannun miyagu yan bindiga dadi yayin da suke tsaka da aikace aikacen gona a cikin gonakansu a kauyen Dapye daga cikin karamar hukumar Wukari ta jahar Taraba.

Shugaban karamar hukumar Wukari, Adigrace Daniel ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru inda ya bayyana sunayen manoman da aka kashe kamar haka; Siman Bala da Timothy Awe.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel