Dame Patience da Aisha Buhari sun hada kai dalilin Maryam Babangida

Dame Patience da Aisha Buhari sun hada kai dalilin Maryam Babangida

Ba kasafai ake ganin matar tsohon shugaban kasa Jonathan, Dame Patience, da Aisha Buhari, uwargidan shugaban kasa, a zaune a karkashin rumfa guda daya ba. Hakan ba abin mamaki bane idan aka yi la'akari da banbancin siyasa da ke tsakaninsu har yanzu.

Patience ta sha yin subutar baki tare da sukar Buhari da kokarin kashe farin jininsa yayin da yake takarar kujerar shugaban kasa tare da mijinta a shekarar 2015.

Amma saboda taron tuna wa da cikar shekaru 10 da mutuwar Maryam Babangida, Aisha da Patience sun gaisa har ma sun zauna tare a wurin taron, wanda aka yi a Abuja.

Ana ganin cewa manyan gidajen biyu, da siyasa ta raba, sun fara sassauta zafin adawarsu tare da yin aiki tare. Ko a cikin da ya gabata sai da Jonathan ya kai wa Buhari wata takaitacciyar ziyara a fadarsa da ke Abuja.

Dame Patience da Aisha Buhari sun hada kai dalilin Maryam Babangida
Dame Patience da Aisha Buhari sun hada kai dalilin Maryam Babangida
Asali: Twitter

Taron wanda Aisha, diyar IBB, ta shirya, ita kuma Aisha Buhari ta kasance mai masaukin baki, ya samu halartar Dolapo Osinbajo, Turai Yar'adua, Jastis Fati Lami Abubakar da sauran wasu manyan mata.

DUBA WANNAN: An kwantar da tsohon ministan Buhari a asibiti, ya nemi 'yan Najeriya su taya shi da add'ua

Maryam Babagida ta mutu ne a ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2009, bayan ta kamu da ciwon dajin mahaifa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel