Biyafara: Trump ya gayyaci Kanu taron gangamin yakin neman zabensa a Amurka

Biyafara: Trump ya gayyaci Kanu taron gangamin yakin neman zabensa a Amurka

A ranar Asabar ne kungiyar 'yan kabilar Igbo masu son balle wa daga Najeriya (IPOB) suka jinjina jam'iyyar Republicans ta kasar Amurka bisa aika gayyata ta musamman ga shugabansu, Nnamdi Kanu.

A ranar Asabar ne aka ga hotunan Kanu tare da wasu shugabanni a kasae Amurka da jagororin jam'iyyar Republicans a wurin taron gangamin yakin neman sake zaben Donald Trump wanda aka yi garin Des Moines a jihar Iowa.

Kungiyar IPOB ta bayyana cewa Kanu ya halarci taron da aka yi ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu, bayan jam'iyyar Republicans ta shugaba Trump ta aika masa katin gayyata na musamman.

A wani jawabi mai dauke da sa hannun sakatarenta, Emma Powerful, kungiyar IPOB ta ce babu yadda za ai kasar Amurka ta gayyaci Kanu taron da Trump zai halarta da a ce shi dan ta'adda ne kamar yadda gwamnatin Najeriya ta ayyana shi.

Biyafara: Trump ya gayyaci Kanu taron gangamin yakin neman zabensa a Amurka
Kanu a wurin taron gangamin yakin neman zaben Trump a Amurka
Asali: Twitter

IPOB ta tabbatar wa da mambobinta cewa za ta hada kai da kasashen duniya masu karfi domin ganin sun cimma burinsu na kafa kasar Biyafra.

DUBA WANNAN: Tsaro: Abinda Buhari ya fada wa shugabannin rundunonin tsaro na kasa yayin ganawarsu

Kungiyar ta caccaki gwamnatin Najeriya da gwamnonin yankin kudu maso gabas a kan bayyana Kanu a matsayin dan ta'adda tare da bayyana cewa babu abinda zai hana su cimma burinsu.

Shugaban kungiyar IPOB, Nnam Kanu, yana cikin jerin masu laifi da gwamnatin tarayya ke nema. Ya tsere daga Najeriya ne bayan kotu ta bayar da belinsa daga tsare shi da ake yi a gidan yari bisa tuhumarsa da laifin cin amanar kasa da tunzura jama'a domin kawo hargitsi da rabuwar kai a kasa.

Tun bayan guduwarsa, har yanzu Kanu bai sake saka kafa a cikin Najeriya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel