Jigo a APC ya tona asirin cin amanar da Ganduje da Abdullahi Abbas suka yi wa jam'iyyar a Kano

Jigo a APC ya tona asirin cin amanar da Ganduje da Abdullahi Abbas suka yi wa jam'iyyar a Kano

Jigo a jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdulmajid Danbilki Kwamanda, ya caccaki gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje, da shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, a kan goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP a zaben maye gurbi da aka yi a karshen makon jiya.

A ranar Asabar ne aka gudanar da zabukan maye gurbi a wasu mazabu da da akwatunan zabe a wasu kananan hukumomin Kano.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da sunan Ali Datti Yako, dan takarar jam'iyyar PDP, a matsayin wanda ya samu nasarar lashe zaben kujerar majalisar wakilai na mazabar Kiru da Bebeji, inda ya kayar da Abdulmunin Jibrin Kofa, dan takarar jam'iyyar APC kuma tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi a majalisar wakilai.

Masana da masu nazarin harkokin siyasar Kano sun yi amanna cewar dattijai da shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano sun hada kai tare da goyon bayan dan takarar jam'iyyar PDP, Ali Datti Yako, bisa sharadin cewa zai sauya sheka zuwa APC bayan zabe.

Masu wannan ra'ayin sun bayyana cewa APC a Kano ta zabi goyon bayan jam'iyyar adawa ne domin nuna wa Abdulmumin kuskurensa na yin rawa irinta siyasa yayin tataburzar zaben gwamnan jihar Kano a tsakanin Ganduje da dan takarar jam'iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Jigo a APC ya tona asirin cin amanar da Ganduje da Abdullahi Abbas suka yi wa jam'iyyar a Kano
Abdullahi Abbas, Ganduje da Ali Datti Yako
Asali: Facebook

A wata hira da aka yi da shi a daya daga cikin gidajen radiyo FM dake Kano, Kwamanda ya bayyana rashin jin dadinsa a kan matakin da jam'iyyar APC ta Kano ta dauka, lamarin da ya kai ga har jam'iyyar ta yi rashin kujerar dan majalisar tarayya.

DUBA WANNAN: Ka cancanci a daureka a kurkuku - Buhari ya mayar da martani ga Sanata Abaribe

Kwamanda, dan gani kashenin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ko kadan bai kamata Ganduje da Abbas su aikata hakan ba saboda biyan bukatar kashin kansu ba, tare da bayyana hakan a matsayin cin amanar jam'iyya da kuma yi mata zagon kasa, wanda a cewarsa hakan kan iya shafar nasarar da APC za ta iya samu a zaben 2023.

"Ina son jan hanakalin mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran shugabannin jam'iyyar APC da su sani cewa mutane suna sane da irin cin amanar jam'iyya da suka yi a mazabar Kiru/Bebeji.

"Idan wani mamba ya yi wa jam'iyya laifi, kamata ya yi a yi a bi hanyoyin da suka dace wajen daukan mataki, maimakon a yake shi lokacin zabe a matsayin hukunci.

"Yanzu 'yan jam'iyya suna ganin cewa Ganduje ya dauki wannan matakin ne saboda ba zai sake yin takarar kujerar gwamna a Kano ba," a cewarsa.

Kazalika, Kwamanda ya bayyana cewa abinda Ganduje da shugabannin jam'iyyar suka aikata, zai iya shafar nasarar APC a Kano a shekarar 2023.

Kwamanda ya yi kira ga uwar jam'iyyar APC ta kasa da ta hukunta Ganduje da Abbas saboda hada kai wajen cin dunduniyar jam'iyya domin kawai su kayar da Kofa tare da bayyana cewa idan ba a yi hakan ba, APC kan iya rasa kujerar gwamna da ta sauran mambobin majalisar tarayya a zaben 2023.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel