Yadda Jeff Bezos wanda ya fi kowa kudi a duniya ya samu dala biliyan 13 a cikin mintuna 15 kacal

Yadda Jeff Bezos wanda ya fi kowa kudi a duniya ya samu dala biliyan 13 a cikin mintuna 15 kacal

- Mamallakin Amazon, kuma babban hamshakin mai kudin duniya, Jeff Bezos ya samu karuwar dala biliyan 13 a dukiyar shi

- Hakan kuwa ya faru ne cikin mintoci 15 da fitar labaran Amazon na watanni ukun karshen shekara kasuwa a ranar Alhamis

- Idan zamu tuna, babban mai arziki kuma dan kasuwa Aliko Dangote ya ce ‘yan Najeriya basu tambayar shi kudi matukar suka hadu sai dai hoton selfie

Mamallakin Amazon kuma babban hamshakin mai kudin duniya, Jeff Bezos ya samu karuwar dala biliyan 13 a dukiyar shi a cikin mintoci 15 kacal. Lamarin da ya kara jaddada zaman shi mutumin da yafi kowa kudi a duniya, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya bayyana.

Bayan sakin labaran Amazon na watanni uku na karshen shekara, an gano cewa su samu shiga kasuwa tare da siyar da su ga mutane na kusan kashi 21 a yayin hutun karshen shekara a ranar Alhamis. Labaran sun daga da kashi 12 cikin dari wanda ya kai shi $2,100 bayan sa’o’in da aka yi ana tallata su. Hakan ya kara wa dukiyar Bezo dala biliyan 12.8 a cikin mintoci 15.

Yadda Jeff Bezos wanda ya fi kowa kudi a duniya ya samu dala biliyan 13 a cikin mintuna 15 kacal
Yadda Jeff Bezos wanda ya fi kowa kudi a duniya ya samu dala biliyan 13 a cikin mintuna 15 kacal
Asali: Facebook

A wannan halin, hamshakin mai kudin na kafada da Bill Gates wajen zama wanda yafi kowa kudi a duniya cikin watannin nan. A halin yanzu, dukiyar shi ta kai dala biliyan 128.9, kamar yadda kiyasin biloniyoyi na Bloomberg ya bayyana.

KU KARANTA: Kirista ya gina Masallatai guda biyu ga matafiya a garin Tafawa Balewa na jihar Bauchi

Idan zamu tuna, a kwanakin baya ne hamshakin mai kudin nahiyar Afirka kuma babban dan kasuwa, Aliko Dangote ya bayyana yadda ‘yan Najerriya basu tambayar shi kudi matukar suka hadu.

Dan kasuwar ya ce sau da yawa ‘yan Najeriya kan bukaci yin hoton selfie da shi ne matukar suka ci karo dashi. Ya ce ya kan fita a cikin ranakun karshen mako don zagayawa cikin birnin Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel