Matana 4 kuma ina alfahari da al'adarmu, ko yanzu aka ce na kara zan karo wasu - Tsohon mai taimakawa shugaban kasa
- Tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Adamu Garba ya ce yana alfahari da auren mace fiye da daya
- Dan siyasar ya ce baya duban mata a matsayin dawainiya, sai dai kuwa babbar kadara
- Kamar yadda ya bayyana, duk da yana da mace fiye da daya, yana fatan samun karin matan auren
Tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC, Adamu Garba ya shiga cikin zantukan da ake yi a kan auren mace fiye da daya a Musulunci.
Matashin ya bayyana cewa yana alfahari da auren mace fiye da daya kuma yana fatan kara aure.
Garba ya bayyana cewa shi kan shi daga gidan da ake auren fiye da mace daya ya fito. Don haka bai amince mace nauyi bace, amma babbar kadara ce.
Dan siyasar ya bayyana cewa yana bukatar karin mata duk da kuwa a halin yanzu yana da mata biyu. Ya ce mata na karo arziki ne, daidaituwa da kuma albarka mai tarin yawa, kamar yadda jaridar Within Nigeria ta ruwaito.
Idan bamu manta ba, Sarki Muhammadu Sanusi II ya bayyana auren mace fiye da daya a matsayin wata hanyar tabbatar da fatara a Arewacin Najeriya. Lamarin da ya jawo cece-kuce daga jama'a da dama.
KU KARANTA: Matar aure ta fadi wanwar bayan mijinta ya nausheta a wajen da aka yi mata tiyatar haihuwa
A ganin wasu hakan ba gaskiya bane don kuwa auren mace fiye da daya na sa a samu arzikin aure wato haihuwa.
Amma kuma wasu na goyon bayan basaraken ganin yadda fatara tayi wa Arewacin Najeriya katutu. Wannan kuwa fatarar ta samu wajen zama ne tun bayan da maza marasa sana'a kwakwara ke tara mata da yawa da kuma haihuwar yaran da ba zasu iya kulawa dasu ba.
Haihuwar yaran na kara musu nauyin dawainiya wanda ke sa wasu iyayen yanke hukuncin tura yaran almajiranci.
Wannan lamarin ya dade yana ci wa gwamnati da wasu jama'a masu kishin al'umma tuwo a kwarya. Suna ganin cewa ajiye mace fiye da daya ba laifi bane, amma tara yara fiye da yadda mutum zai iya daukar dawainiyarsu ne babban aibun.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng