Maimuna: Yarinyar da ta tsira daga hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta a Katsina

Maimuna: Yarinyar da ta tsira daga hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta a Katsina

Maimuna Abdulmumin yarinya ce da aka yi wa auren wuri kuma aka yanke mata hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An aurar da Maimuna tana da shekaru 13 a duniya amma mijinta ya mutu bayan watanni biyar wanda ake zargin ta da kisan shi. An kama ta bayan wannan harin da yayi sanadiyyar mutuwar mijinta amma an dakata har zuwa bayan shekaru biyu kafin a tuhumeta da wani laifi.

A cikin shekaru biyun, ta kara aure har da rabon haihuwa. Bayan shekaru shida da mutuwar mijinta na farko, an yanke mata hukuncin kisa bayan shaidu sun bayyana cewa ita ta kashe mijinta a ranar 6 ga watan Disamba, 2012.

Ta dau shekaru uku a gidan gyaran hali na jihar Katsina. Kamar yadda shari'ar Maryam Sanda ta jawo hankulan kungiyoyi daban-daban na duniya, haka shari'ar Maimuna ta jawo lauyoyi daga Avocats Sans Frontieres tare da wasu lauyoyin a duniya.

Maimuna: Karamar yarinyar da ta tsira daga hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta
Maimuna: Karamar yarinyar da ta tsira daga hukuncin kisa bayan ta kashe mijinta
Asali: Twitter

Sun fara aiki tare da fatan ayi wa karamar yarinyar adalci a kan wannan hukuncin na kisa wanda ya ci karo da dokokin kare hakkin dan Adam na duniya. Dokar ta ce ba za a iya yankewa mutum mai kasa da shekaru 18 hukuncin kisa ba.

Kamar yadda takardar da jaridar ThisDay ta fitar a ranar 13 ga watan Satumba, 2016, "Bayan kara duban shari'ar Maimuna da kotun ECOWAS tayi a 2014, ta umarci gwamnatin Najeriya da ta biya ta miliyan 6 na tarar hukuncin kisa da aka yanke mata a laifin da ta aikata tana karama. Amma kuma gwamnatin bata cika wannan sharadin ba."

DUBA WANNAN: Mai wa'azin addinin Kirista ya nemi gafara kan kalaman batanci da ya yi game da Musulunci

An sauke hukuncin kisan da aka yankewa Maimuna a kotun daukaka kara.

Angela Uwandu, shugabar babban ofishin Avocats San's Frontiers France ta yi martani bayan sakin Maimuna. Ta ce "Duk da an dade kuma an jigata kafin a samar da adalci ga Maimuna, an samu kubutar da ita. Muna matukar farin ciki da Maimuna ta koma cikin danginta."

Abinda Maimuna ta fuskanta na daya daga cikin abinda mutane da yawa ke fuskanta wadanda basu da wanda zai tashi tsaya a kansu. Hakan kuwa na nuna gazawar shari'a a kan kananan yara a Najeriya.

Wannan ya tuna mana shari'ar Wasila Umar wacce aka yi wa auren wuri kuma ta kashe mijinta a 2014 a jihar Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel