Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana

Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana

- Jami'an hukumar jiragen ruwa ta kasar Ghana sun kama wasu 'yan Najeriya wadanda suka shiga cikin kaya ba tare da an sani ba suka sauka a Ghana

- 'Yan Najeriyar a tunaninsu jirgin ruwan zai kare tafiyar shi ne a kasar Spain amma ashe hasashensu ba gaskiya bane

- Tuni dai aka damka su a hannun 'yan sanda tare da kayen maye, kayan abinci da kuma gudumar da aka kama su da ita

Jami'an hukumar jiragen ruwan kasar Ghana sun kama wasu 'yan Najeriya uku da suke sulale tare da shigewa cikin wani jirgin ruwa wanda suke tsammanin zai tashi daga Apapa ne zuwa kasar Spain.

Wadanda ake zargin masu fatan su sauka a kasar Spain don neman arziki, an gano sunayensu da: Daniel mai shekaru 32, Stephen Nuta mai shekaru 28 da Kelvin Popoola mai shekaru 26. An kama su ne a wani karamin wuri kusa da fankar jirgin bayan an tsayar dashi a kasar Ghana don sauke wasu mata a Tema da ke Ghana, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana
Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana
Asali: Facebook

An kama wadanda ake zargin da kayan maye, kayan abinci da kuma guduma, wadanda suke hannun 'yan sanda tare da mutanen uku a tsare.

Daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Daniels an taba kama shi a 2019 kuma aka dawo dashi Najeriya da wani sunki na $600.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Allah ya haramtawa mace tayi bincike a wayar mijinta - Cewar wani soja

Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana
Biyu babu: 'Yan Najeriya da aka yiwa karyar za a kai su Turai sun tsinci kansu a kasar Ghana
Asali: Facebook

Mutane dai irin wadannan basu da wuyar yaudara in suka fada hannun miyagun mutane.

Irinsu ne kan fada hannun masu safara da siyar da jama'a wadanda ke musu karyar zasu kaisu kasashen Turai don nemo arziki. Daga baya kuwa su kare a wasu kasashen Afirka inda ake siyar dasu don bauta.

Idan kuwa mata ne, sau da yawa sukan koka idan an siyar dasu don nemawa wasu kudi ta hanyar karuwanci. A kan ci zarafinsu duk ta yadda aka so inda daga baya idan da rabo suke komowo gida Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel