Yadda na yi wa Kwankwaso ritayar dole a siyasa - Ganduje

Yadda na yi wa Kwankwaso ritayar dole a siyasa - Ganduje

Gwamna Abdullahi Ganduje bayyana nasarar da jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta samu a zaben maye gurbin da aka kammala a jihar a matsayin alama da ke nuna cewa an yi wa tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ritaya daga siyasa.

Sanarwar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Juma'a ya ce gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke maraba da Kakakin majalisar jihar, Abdulaziz Gafasa da wasu manyan masu rike da mukamai a majalisar da suka raka sabbin 'yan majalisun jihar hudu zuwa gidan gwamnati.

A cewar Ganduje, nasarar da ya samu a kotun koli ta sake tabbatarwa cewa Rabiu Kwankwaso ya yi ritaya daga siyasa.

Yadda na yi wa Kwakwaso murabus daga siyasa - Ganduje
Yadda na yi wa Kwakwaso murabus daga siyasa - Ganduje
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

"A shekarun baya kokacin da shi (Kwankwaso) ke shirin takarar kujerar shugaban kasa, ya yi ta cika bakin cewa zai yi wa Shugaba Buhari ritaya daga siyasa. Ya ce nima zai min ritaya. Amma idan ka duba yanzu, wanene aka tilastawa yin ritaya?," in ji Ganduje.

Ya cigaba da cewa, "Dan majalisar jiha mai wakiltan Madobi da Dan majalisar wakilai daga yankin, da shugaban karamar hukuma da kansiloli da Sanata mai wakiltan Madobi da gwamnan jiha duk 'yan jam'iyyar APC ne. Shin wannan ba alama ba ce da zai nuna masa cewa mun masa ritaya daga siyasa?"

A yayin da ya ke Allah wadai da irin kalame da halayen da tsohon gwamna Kwankwaso ya rika nuna wa musamman yayin zabe, Gwamna Ganduje ya ce mu irin tsarin siyasar mu cikin mutunci da lissafi mu ke yi.

Ganduje ya yi kira ga zababun 'yan majalisar jihar su kasance masu mutunta shugabannin jam'iyyar kuma su kasance masu biyaya ga jam'iyya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel