Kunar bakin wake ya dawo a Maiduguri: Karamar yarinya ta kashe mutane 3 a Islamiyya

Kunar bakin wake ya dawo a Maiduguri: Karamar yarinya ta kashe mutane 3 a Islamiyya

Wata karamar yarinya yar shekara 12 ta tashi bamabamai a cikin wata makarantar Islamiyya a jahar Borno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kananan yara maza guda uku, tare da raunata wasu mutane hudu.

Jaridar Punch ta ruwaito wani sojan sa kai ne ya tabbatar harin, inda yace lamarin ya auku ne da yammacin ranar Alhamis a wata makarantar islamiyya dake garin Muna Dalti, wajen garin Maidugurin jahar Borno.

KU KARANTA: An kashe mutane 3, an babbaka gidaje 20 saboda rikicin sarauta a jahar Kogi

Matashin Sojan sa kai mai suna Mohammed Bola ya bayyana cewa: “Kai tsaye yarinyar ta wuce cikin daliban a daidai lokacin da suke tashi daga karatu, nan take ta tashi kanta a tsakiyansu, ta kashe yara 3, guda hudu kuma suka jikkata.

Majiyarmu ta ruwaito ko kafin aukuwar wannan hari, wata yar karamar yarinya ma ta kai kwatankwacin wannan hari a wani gida dake garin Muna Dalti, inda ta lalata gidan gaba daya, amma babu wanda ya mutu, sai dai ta jikkata wani mutum daya.

A wani labarin kuma, akalla mutane uku ne suka mutu a sakamakon wata rikita rikita da ta kunno kai a kan wata kujerar sarauta a cikin karamar hukumar Ankpa ta jahar Kogi, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu gidajen sarauta guda biyu ne suke jayayya a kan wannan kujerar sarauta wanda aka dade ana zaban wanda zai hauta a tsakaninsu, toh amma a wannan karo lamarin ya ta’azzara, har ta kai ga zubar da jini da asarar dukiya.

Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya fara ne a daren Laraba, 29 ga watan Janairu a kan wannan kujerar sarauta ta ‘Onu Akwu’, sai dai ba daga ranar aka fara jayayyar ba, sun dade kowa na ikirarin lokacinsa ne ya fitar da sarki, wanda har ta kai su ga kotu.

“Muna cikin barci sai muka ji hayaniya daga yankin gabashin garinmu, a lokacin da na fito sai na tarar wasu gidaje suna ci da wuta.” Kamar yadda wani mazaunin garin, kuma ganau ba jiyau bay a bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel