2023: PDP ta bayyana sabuwar dabarar da za tayi amfani da shi domin kwace mulki daga hannun APC

2023: PDP ta bayyana sabuwar dabarar da za tayi amfani da shi domin kwace mulki daga hannun APC

- Jam'iyyar PDP ta ce ta fara shirya tsare-tsarenta a kan zabukan 2023 da ke gabatowa don ture gwamnatin APC

- Uche Secondus, shugaban jam'iyyar ya ce a shirye suke don yin maja wacce za ta kara karfafa jam'iyyar

- Shugaban jam'iyyar ya ce babu wani dan jam'iyyar da zasu hana shiga jerin neman tikitin takarar shugaban kasa, koda kuwa ba daga yankin da suke so bane

Jama'a da yawa na kallon 2023 a wani dogon lokaci, amma banda 'yan siyasar Najeriya. Watanni kalilan bayan zaben 2019, an fara shiri da tsari na zabe mai zuwa.

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta bayyana tsare-tsarenta na zaben 2023 ta yadda za ta hankade gwamnatin jam'iyyar APC.

Kamar yadda shugaban jam'iyyar APC na kasa, Uche Secondus ya bayyana, jam'iyyar PDP ta shirya don yin maja wacce za ta karfafa jam'iyyar wajen ture APC daga mulki.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Secondus ya ce babbar jam'iyyar adawar na shiri tare da tsarin ture APC warwas a zabe mai zuwa.

2023: PDP ta bayyana sabuwar dabarar da za tayi amfani da shi domin kwace mulki daga hannun APC
2023: PDP ta bayyana sabuwar dabarar da za tayi amfani da shi domin kwace mulki daga hannun APC
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Maciji ya kashe wani mai wasa da macizai yayin da ya ke nuna bajintarsa (Bidiyo)

Shugaban jam'iyyar PDP din ya ce tikitin takarar shugaban kasa a 2023 na jam'iyyar zai je hannun kowanne dan jam'iyyar ne da ya cancanta ba tare da duban yankin da dan takarar ya fito ba.

Hakazalika, Secondus ya musanta yuwuwar sauya sunan jam'iyyar. Ya zargi gwamnatin APC da ba 'yan Najeriya kunya. Ya ce laifin matsalar tsaro, rashawa, yunwa, wargajewar tattalin arziki da fatara duk APC ce ta jawo.

Amma kuma, dattijon Najeriya mai suna Chief Bode George ya ce ya mallaki duk abinda ake nema ta fannin ilimi da gogewa da zasu sa ya mulki kasar nan a 2023.

Chief George, wanda tsohon mataimakin jam'iyyar PDP ne na kasa ya ce nan ba da dadewa ba zai bayyana matsayarsa a kan fitowa takara a 2023. Dattijon ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 29 ga watan Janairu 2020, a jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel