Najeriya ta zama 29 a duniya sannan ta 3 a Afrika cikin kasashen da suka fi iya turanci

Najeriya ta zama 29 a duniya sannan ta 3 a Afrika cikin kasashen da suka fi iya turanci

- 'Yan Najeriya ne suka zama na 29 a cikin jerin mutanen duniya da suka kware a turanci

- Kasar Afirka ta Kudu ce ta daya a nahiyar Afirka yayin da kasar Kenya ke biye da ita

- A cikin birane kuwa, birnin Nairobi ne na daya a duniya inda birnin Legas ke biye da shi

Wannan jerin an fitar da shi ne bayan da aka yi gwajin kwarewa a turanci ga wadansu tarin mutane na kasashen duniya. A nahiyar Afirka, 'yan Najeriya ne na uku da suka fi iya sarrafa yaren turanci a harshensu kamar yadda rahoton global private language tutor, Education First (EF) suka bayyana.

Najeriya ce ta zo a ta 29 a duniya inda kasar Afirka ta kudu ta bayyana a ta 6 a duniya baki daya.

EPI din da kamfanin kasar Switzerland yayi ya sa kasar Kenya a bayan ta Afirka ta Kudu duk da cewa Nairobi ne ya zo birnin da aka fi iya turanci a nahiyar Afirka.

Najeriya ta zama 29 a duniya sannan ta 3 a Afrika cikin kasashen da suka fi iya turanci
Najeriya ta zama 29 a duniya sannan ta 3 a Afrika cikin kasashen da suka fi iya turanci
Asali: Facebook

Najeriya ce ta uku bayan kasar Afirka ta kudu da Kenya a fadin nahiyar Afirka baki daya. Kiyasin ya bayyana kashi 50.26 na mutanen kasar na jin turanci mai kyau.

Sauran kasashen Afirka da suka bayyana a jerin kasashe 100 na duniyan sun hada da kasar Ethiopia wacce ta zo a ta 63, kasar Tunisia ta zo a ta 65, kasar Egypt ta 77, kasar Kamaru ta bayyana a ta 83, kasar Sudan a ta 87, kasar Algeria ta zo a ta 90, kasar Ivory Coast a ta 96 da kuma Libya ta 100.

KU KARANTA: Ga irinta nan: An yanke masa hukuncin daurin rai da rai bayan ya yiwa 'yar uwar matarshi fyade

Kasashen duniya da suka zo a saman jerin sun hada da kasar Netherlands wacce ke biye da Sweden, Norway, Denmark da Singapore.

Kenya ta samu kaso mai yawa wanda ya kai kashi 60.51 amma kuma Netherlands da ke kan gaba na da kashi 70.27.

A kuma bangaren biranen da aka fi iya turanci, Nairobi ya bayyana a kan gaba a Afirka da kaso 61.94 wanda birnin Legas ke biye da kashi 58.47.

Wannan binciken na EF din ya danganta kwarewa a turanci da kirkire-kirkire, saka hannayen jari a bincike da ci gaba, yawan masu bincike da sauransu. An samu sakamakon ne bayan da manyan mutane miliyan 2.3 suka shiga wannan gwajin da aka yi a yanar gizo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel