Gwamnonin Kudu maso gabas za su kafa hukumar tsaro a yankinsu

Gwamnonin Kudu maso gabas za su kafa hukumar tsaro a yankinsu

- Biyo bayan kafa hukumar tsaro na Amotekun a yankin Kudu maso yamma, jihohin Kudu maso gabas su ma za su kafa ta su hukumar tsaron

- Shugaban gwamnonin yankin na Kudu maso gabas, Gwamna Umahi ya ce tuni sun rubuta wasikar neman izini ga gwamnatin tarayya kuma sun tattauna da shugabanin hukumomin tsaro

- Gwamnan na jihar Ebonyi ya ce hakan ya zama dole saboda kiyaye rayuka da dukiyoyin mutanen da ke yankinsu

Gwamnan jihar Ebonyi kuma shugaban kungiyar gwamnonin yankin Kudu maso Gabas ya ce yankin ta kafa hukumar tsaron ta domin kare lafiya da dukiyoyin al'ummar ta.

Da ya ke karbar bakoncin babban kwamandan 82 Divison na sojojin Najeriya, Lasisi Adegboye a Abakaliki babban birnin jihar, gwammnan ya ce kungiyar ta rubutawa gwamnatin tarayya wasikar neman izinin kafa hukumar.

Gwamnonin Kudu maso gabas za su kafa hukumar tsaro a yankinsu
Gwamnonin Kudu maso gabas za su kafa hukumar tsaro a yankinsu
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Diyar gwamnan Bauchi ta yi wa masu fakewa da hukuncin Maryam Sanda suna yi wa musulunci batanci raddi

"Ko wace yanki tana da nata irin matsalolin da suka damun ta kuma mu ma mun kafa ta mu hukumar tsaron kuma mun rubutawa gwamnatin tarayya wasika neman izini mun fara shirye-shirye domin mun gana da shugabanin hukumomin tsaro," in ji Umahi.

"Mun tattauna a kan abinda za muyi da matakin da za mu dauka domin cigaba da kiyaye mutanen mu a yankin Kudu maso gabas.

"Babu wanda zai ce zai shiga tsarin tsaro na hadin gwiwa ba domin ana iya sace mutum a jihar Anambra kuma daga bisani a tsince shi a jihar Ebonyi.

"Saboda haka akwai bukatar mu hada karfi da karfe domin ganin mun kare kowa kuma mu a nan Ebonyi, muna daga cikin wadanda suka fara kafa hukumar tsaro ta cikin gida wanda muke kira Neighbourhood Watch kuma kawo yanzu aikinsu yana kyau sosai."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel